'Aminu Ado Bayero a Makabarta Yake Zaune ba Fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

'Aminu Ado Bayero a Makabarta Yake Zaune ba Fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

  • Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kore kima da darajar wurin da Alhaji Aminu Ado Bayero ya tare bayan cire masa rawani
  • Ana yiwa wurin kallon fada amma sakataren yada labaran gwamnatin Kano ya ce makabarta ce mai tarihi da ke neman gyara
  • Sanusi Dawakin Tofa ya ce amfanin gidan Nassarawa shi ne birne sarakunan Kano ko masaukin manyan bakin sarki

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamnatin Mai girma Abba Kabir Yusuf ta kafe a kan zancen dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Babban sakataren yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya hakikance a kan rusa masarautun da aka kirkiro.

Aminu Ado Bayero
Aminu Ado Bayero da wasu fadawa a gidan Nassarawa a Kano Hoto: @HRHBayero
Asali: Twitter

"Aminu Ado ya tare a makabarta" - Gwamnati

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abba Kabir ya magantu kan mutuncin Aminu Ado, ya fadi masu zuga shi

A wata hira da aka yi da shi a tashar Arise, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya zargi Aminu Ado Bayero da jefa kan shi a cikin kunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun bakin gwamnan na Kano ya yi zancen ne da aka bijiro da zancen rusa bangaren karamar fadar Sarki ta Nassarawa.

Sanusi Dawakin Tofa ya ci gyaran jama’a, yake cewa Aminu Ado Bayero yana zaune ne a makabarta ba fada kamar yadda ake tunani ba.

Gwamna Abba ya fadi amfanin gidan Nassarawa

A cewarsa, gidan Sarkin da ke Nassarawa wuri ne da ake birne sarakunan Kano da suka rasu, ba fada ba ce da Sarki zai tare a cikinta.

Bayan birne sarakai, hadimin gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce a kan yi amfani da gidan wajen sauke manyan bakin Sarki a jihar Kano.

Kara karanta wannan

‘Burgar banza’: Hadimin Ganduje ya takalo Abba kan yunkurin fatattakar Sarki Aminu

Zuwa yanzu, Dawakin Tofa ya ce an birne sarakuna akalla hudu a makabartar, daga ciki har da Marigayi Ado Bayero da ya rasu a 2014.

Idan Mai alfarma Sarkin Musulmi ko wani babban basarake ya ziyarci Kano, a wannan gida ake sauke shi a maimakon a kai shi otel.

Wani amfani na gidan shi ne Mai martaba Sarkin Kano ya kan zauna a ciki ya huta ranar hawan Nassarawa kafin ya shiga gidan gwamnati.

Abba: "Sanusi II zai bukaci gidan Nassarawa"

Dawakin Tofa ya ce a yanzu Sarki Muhammadu Sanusi II zai cigaba da amfani da fadar, shiyasa ake bukatar a gyara shi domin ya tabarbare.

Kakakin gwamnan ya yi ikirarin sun damu da halin da Alhaji Aminu Bayero ya tare a wurin da ya ke bukatar gwamnatin Kano ta gyara shi.

A hirar da aka yi, mai magana da yawun gwamnan ya ce Sarki na 15 ne ya kawo kan shi wurin ya zauna, babu wanda ya hana shi yawatawa.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

An karawa Aminu Ado Bayero tsaro

Labari ya zo cewa an kara jibgewa Mai martaba Aminu Bayero jami’an tsaro alhali kuwa gwamna Abba Kabir Yusuf na neman a fitar da shi.

Tsohon ‘dan takaran gwamnan Kano, Salihu Yakasai ya fadi halin da ake ciki a fadar Nassarawa, ya ce ba abin da zai faru da Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng