Sarkin Musulman Najeriya: Wanene Sultan, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III?

Sarkin Musulman Najeriya: Wanene Sultan, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III?

A makon nan ne Mai alfarma Sarkin Musulman Najeriya, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya cika shekaru 64 a Duniya.

Legit.ng Hausa ta kawo maku takaitaccen tarihin Muhammadu Sa’ad Abubakar III wanda ya gaji iyayensa a kan sarautar Sarkin Musulmai.

Sa’ad Abubakar III ya bi tafarkin mahaifinsa, ya yi karatun boko, kuma ya shiga gidan soja inda har ya rike mukamai masu muhimmanci.

Wanene Muhammad Sa’ad Abubakar III?

1. Haihuwa

An haifi Muhammadu Sa'ad Abubakar III ne a ranar 24 ga watan Agusta, 1956. Shekararsa 64 yanzu da haihuwa. Shi ne ‘Dan auta cikin ‘ya ‘yan Marigayi Sarkin Musulmi Abubakar III

2. Karatun boko

Sa’ad Abubakar III ya halarci shararriyar makarantar sakandaren nan ta Arewa watau Barewa College da ke Zariya.

Bayan ya kammala karatun sakandare, ya zarce zuwa makarantar zama soja ta NDA da ke garin Kaduna a shekarar 1975.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya ziyarci Kaduna, ya gana da Gwamna El-Rufai

Sarkin Musulman Najeriya: Wanene Sultan, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar?
Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar a wajen taro
Asali: Facebook

3. Gidan Soja

A shekarar 1977, Sa’ad III ya samu cikakken horaswa, ya fito daga gidan soja a matsayin Laftana, ya rike manyan mukamai.

Sultan ya shugabanci dakarun da ke gadin fadar shugaban kasa a lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya ke mulkin Najeriya.

Sa’ad III ya jagoranci dakarun OAU da ECOMOG wajen kwantar da tarzoma, ya rike mukami a lokacin da ya ke cikin dakarun ECOWAS.

Aikin karshe da Sultan ya yi a gidan soja shi ne Jakadan tsaro zuwa Fakistan da wasu kasashe.

4. Sarkin Musulmi

A Nuwamban 2006, Sa’ad Abubakar III ya zama Sultan bayan ‘danuwansa Muhammadu Maccido ya rasu a hadarin jirgin sama.

Muhammadu Sa’ad Abubakar III ya shafe kusan shekaru 14 a kan gadon kakansa, Shehu Danfodio.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel