Rikicin Sarauta: Gwamna Abba na Cikin Matsala, An Bayyana Sahihin Sarkin Kano

Rikicin Sarauta: Gwamna Abba na Cikin Matsala, An Bayyana Sahihin Sarkin Kano

  • Wani mai sharhi kan harkokin al'umma, Law Mefor ya ce duba da hukuncin babbar kotun tarayya, Sanusi ya rasa kujerar sarautar Kano
  • Mefor ya ce duk da kotun koli ta haramtawa manyan kotunan tarayya sa baki a sha'anin sarauta, bai kamata gwamnati ta ƙi mutunta umarnin doka ba
  • Ya ce mai shari'a Abdullahi Liman ya umarci kowa ya koma matsayinsa na kafin sabuwar dokar masarauta ta 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Law Mefor, fitaccen mai sharhi kan al'amuran yau da kullumal ya ce gwamnatin jihar Kano ba ta ikon sauya hukuncin da kotu ta yanke.

Mefor ya bayyana cewa idan gwamnatin Abba Kabir tana da ja da hukuncin babbar kotun tarayya, kamata ya yi ta ɗaukaka ƙara ba wai ta take umarnin doka ba.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu: Hadimin gwamna da fitaccen lauya sun samu saɓani kan hukuncin kotu

Aminu Ado Bayero da Sanusi II.
Aminu vs Sanusi: Fitaccen mai sharhi ya fadi sahihin Sarkin Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Totori Master
Asali: Twitter

Idan baku manta ba babbar kotun tarayya ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da kotu ta yanke

A ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, Mai shari'a Abdullahi Liman ya soke duka matakan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka bayan kafa sabuwar dokar masarauta.

Alkali Liman ya ce hukuncin bai shafi dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da ita ba.

Amma ya soki Gwamna Abba bisa yadda ya zartar da dokar kuma ya mayar da Sanusi II a watan Mayu duk da kotun ta umarci ya jinkirta.

Law Mefor ya soki gwamnan Kano

Da yake martani kan ruɗanin sarautar Kano a wata hira da Arise tv, Mefor ya ce:

"Kotun ɗaukaka ƙara ce kaɗai ke da hurumin jingine umarnin kotu ko ta tabbatar da shi, ba gwamnan jihar Kano ba. Amma gwamnan ya sa ƙafa ya shure umarnin kotu.

Kara karanta wannan

"Ba a sauke Sanusi II ba," Gwamnatin Kano ta yi ƙarin haske kan hukuncun kotu

"Haka majalisar dokokin jihar ta mara masa baya, suka zartar da wannan doka ta masarauta, wanda yanzu tana kasa tana dabo."

Hadimin gwamna a ƙauya sun shiga ruɗani

A wani rahoton na daban hukuncin babbar kotun tarayya a shari'ar sarautar Kano ya haddasa saɓani tsakanin hadimin gwamna da lauya Abba Hikima.

Mai magana da yawun Abba Kabir ya ce hukuncin ya rusa masarautu biyar yayin da Hikima ke ganin har yanzu Aminu Bayero ne Sarkin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262