Abubuwa 10 da Suka Faru da Sanusi II Tun da Ya Koma Karaga a Tsakiyar Rikicin Sarauta
Kano - Abubuwa da-dama sun faru da Muhammadu Sanusi II daga lokacin da aka maido da shi kan karagar mulki zuwa yau.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
A wannan rahoto, Legit ta shiga masarautar ta Kano mai dinbin tarihi domin tattaro abubuwan da aka yi cikin wata guda.
1. Sanar da nadin Muhammadu Sanusi II
A ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu 2024, Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa Muhammadu Sanusi II ya dawo mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Yusuf ya dauki matakin bayan sa hannu a dokar masarauta ta shekarar 2024. Daily Trust ta kawo wannan labari lokacin.
2. Mikawa Sarki Sanusi II takarda
Washegari sai gwamna Abba Kabir Yusuf ya mikawa Khalifa Muhammadu Sanusi II takardar nadi a matsayin Sarkin Kano.
3. Shiga fadar Sarkin Kano
Bayan awanni sai manyan jami’an gwamnatin Kano su ka yiwa Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II rakiya zuwa fada.
A wannan lokaci Alhaji Aminu Ado Bayero yana kan hanyar dawowa daga tafiya da ya yi.
4. Sanusi ya yi limancin sallar Juma’a
Khalifan na darikar Tijjaniya kuma Martaba Sarki ne ya jagoranci sallar Juma’ar farko da ya yi a masallacin Sarki da ke Kofar Kudu.
A hudubar da ya gabatar, an ji Sarki ya yi maganar muhimmancin imani da kaddara.
5. Umarni dabam-dabam daga kotu
Daga nan kotu suka rika ba da umarni mabanbanta kan rikicin masarautar. Mai shari’a Aisha Adamu Aliyu ta ce a kori Aminu Bayero.
Can kuma sai aka ji kotun tarayya ta ba da hukuncin korar Sarkin Kano daga cikin fadar kamar yadda Leadership ta tattaro labarin.
6. Sarki Sanusi II ya karbi mubaya’a a Kano
Bayan abubuwa sun soma lafawa, Sarki Sanusi II ya fara karbar gaisuwa daga talakawa da kuma mubaya’a daga wajen hakiman Kano.
Mafi yawan hakimai sun yi mubaya’a ga sabon sarkin da aka dawo da shi a nan ne kuma aka samu sabani daga gidan Sheikh Dahiru Bauchi.
7. Fito da fai-fen murya
Ana haka sai ga wani fai-fai yana yawo inda wasu suka yi ikirarin Mai martaba ne yake waya da wani kafin dawo da shi kan karaga.
Masoya sun ce kirkirar sautin aka yi da fasahar zamani ko akalla kwaikwayon muryar.
8. Wasika daga dangin Inyass
Ba a gama wannan ba kuma sai ga wata wasika da aka yi ikirari ta fito ta hannun Sheikh Mahe Niasse a madadin gidan Ibrahim Inyass.
Wannan wasika da daga baya aka gano ta karya ce, ta yi kira ga Sarki ya hakura da sarauta, ya yi koyi da kakansa Muhammadu Sanusi II.
9. Shirin hawa sallah a Kano
Ana shirye-shiryen bikin idi ne kuma sai ‘yan sanda suka fitar da sanarwar haramta hawa sallah. Hakan ya takawa har Aminu Ado Bayero burki.
10. Hukuncin kotu kan rikicin sarauta
Kotun tarayya ta zartar da hukuncin da ya bata dukkan matakan da Abba Kabir ya dauka bayan ya rattaba hannu a sabuwar dokar masarauta.
Sanusi II ne Sarki ko Aminu?
Bayan hukuncin kotu, amsa ta fito a kan wanene sahihin Sarkin Kano ta fuskar doka kamar yadda aka ji labari Abba Hikima ya fayyace batun.
Barista Abba Hikima ya ce har gobe Alhaji Aminu Ado Bayero yana kan karagar mulki domin alkali ya dakatar da aiki da sabuwar doka.
Asali: Legit.ng