"Kar Ku Damu," Rundunar Sojoji Ta Dauki Alkawarin Kare Manoma Daga 'Yan Ta'adda

"Kar Ku Damu," Rundunar Sojoji Ta Dauki Alkawarin Kare Manoma Daga 'Yan Ta'adda

  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta shaidawa manoman kasar nan cewa su kwantar da hankalinsu domin za a ba su kariya da zai ba su damar yin noma a gonakinsu dake fadin kasar
  • Daraktan ayyukan yada labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, inda ya ce rundunar sojojin kasar nan ta yi garanbawul da ayyukanta
  • Manoma a Najeriya, musamman wadanda ke Arewacin kasar nan na fusknatar barazanar tsaro daga yan ta’addan dake tilasta ma su biyan haraji kafin su shiga gonakinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hedikwatar tsaro ta Najeriya (DHQ) ta kwantar wa da manoman kasar nan hankali, inda ta ce ta yiwa ayyukanta garanbawul yadda zai ba ta damar tsare rayukansu idan za su je gona.

Kara karanta wannan

Sojoji sun tarwatsa 'yan ta'adda suna shirin taron kitsa manakisa a Kaduna, an kashe miyagu

Alkawarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma, musamman a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara ke fuskantar barazana daga yan ta’adda na biyan haraji kafin su shiga gona.

Defense Headquarters Nigeria
Sojoji za su kare manoma a bana Hoto: Defense Headquarters Nigeria
Asali: Facebook

Leadership News ta wallafa cewa darektan ayyuka na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar noman bana da manoma a sassan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna murkushe yan ta’adda,’ Sojoji

Hedikwatar tsaron kasar nan ta ce tana samun nasara sosai wajen dakile ta’addanci da kama ‘yan ta’adda da dama da suka addabi ‘yan Najeriya.

Darektan ayyukan yada labarai na hedikwatar, Manjo janar Edward Buba ya shaidawa manema labarai cewa a cikin mako guda, sun kashe yan ta’adda 220, an kuma kama wasu 395.

Daga nasarorin da sojojin Najeriya su ka samu akwai ceto mutane 202 da aka yi garkuwa da su, tare da kwace mugayen makamai daga hannayensu.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

An samu nasarorin ne a jihohi da dama ciki har da Borno, Binuwai da Kogi kamar yadda rundunar sojojin kasar nan ta wallafa a shafinta na Facebook.

Manjo janar ya ce dakarunsu za su kara jajircewa wajen matsawa yan ta’adda a kasar nan har sai an kakkabe ta’addanci tare da wanzar da zaman lafiya.

An kashe barayin daliban Kuriga

A wani labarin kun ji cewa sojojin Najeriya da taimakon sauran jami’an tsaro sun kashe wasu daga cikin yan ta’addan da su ka sace daliban makarantar Kuriga 137 da ke jihar Kaduna.

Sojojin sun yi nasara ne a lokacin da su ke kokarin ceto daliban da aka sace a Kaduna, aka kuma nausa da su jihar Zamfara, inda a nan ne aka samu ceto su baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.