Jerin Kasashe 5 da Suke Bin Najeriya Bashi da Zunzurutun Kudaden da Suke bi, China ce Kan Gaba

Jerin Kasashe 5 da Suke Bin Najeriya Bashi da Zunzurutun Kudaden da Suke bi, China ce Kan Gaba

  • Wannan kiyasin yayi dogaro ne da abinda ofishin kula da bashi suka wallafa a shafinsu na yanar gizo, hukumar kula da kiyasin bashi na kasar nan
  • Duk da bayanan yarjejeniyar Najeriya da China ba su bayyana ba, bayanan DMO sun nuna cewa kasashe biyar ke bin Najeriya zunzurutun bashin sama da N1 tiriliyan
  • Kamar yadda ake tsammani, China ce kasar da ke kan gaba a fannin yawan basussukan da kasashen ke bin Najeriya kuma an samu bashin ne ta hanyar yarjejeniya

Kamar yadda bayanan da aka samu daga ofishin kula da basussuka, kasashen duniya biyar ne ke bin Najeriya zunzurutun kudi har $4.49 biliyan wanda yayi daidai da N1.91 tiriliyan idan aka canza dala kan N430 a watan Maris na 2022.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Sojoji sun gano dan ta'addan da ya kitsa kai hari kan tawagar Buhari a Daura, sun sheke shi

Kasashen da Najeriya ta dinga rancen kudi cikin shekarun nan sun hada da Faransa, China, Japan, Indiya da Jamus.

Baba da China
Jerin Kasashe 5 da Suke Bin Najeriya Bashi da Zunzurutun Kudaden da Suke bi, China ce Kan Gaba. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An samu basussukan daga kasashen ne ta hanyar yarjejeniya tsakanin kasashen da Najeriya.

Nawa kasashen ke bin Najeriya?

Kamar yadda ake tsammani, tsagwaron kudin da China take bin Najeriya, kasancewarta kasar da ke kan gaba wurin bin Najeriya bashi, ya kai $3.66 biliyan ko kuma N1.55 tiriliyan.

Yayin da Najeriya ta ranci kudi daga Faransa ta hannun Agence Franchise Development har $567.89 miliyan wanda yayi daidai da 241.63 biliyan.

Gwamnatin tarayya ta kara da cin bashin $67.96 wanda yayi daidai da N28.91 biliyan daga kasar Japan ta hannun Japan International Cooperation Agency.

Ta kara da cin bashin Indiya $28.33 miliyan ta Exim Bank of India tare da kasar Jamus ta hannun Kreditanstait Fur Wiederaufbua har $164.04 miliyan.

Kara karanta wannan

Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

‘Danuwan Buhari ya Fadawa Duniya Wanda ya yi Dalilin Barinsa Jam’iyyar APC

A wani labari na daban, Fatuhu Muhammed, mai wakiltar Daura/Sandamu/Mai Adua a majalisar wakilan tarayya ya fadi abin da ya jawo ya sauya-sheka daga APC.

A ranar Litinin, 8 ga watan Agusta 2022, Daily Trust ta rahoto Honarabul Fatuhu Muhammed ya na bayanin yadda abokin adawa ya ci masa mutunci.

Da aka zanta da shi a ranar Lahadi, ‘dan siyasar yace abokin takararsa a zaben fitar da gwani, ya zagi mahaifinsa ne, a dalilin haka shi ya canza sheka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel