Kotu ta Daure Matashin da Ya Sace Dabbobi, ya Kalmashe Kudin Mutane a Aljihu

Kotu ta Daure Matashin da Ya Sace Dabbobi, ya Kalmashe Kudin Mutane a Aljihu

  • Wani matashi mai shekaru 35 ya gamu da fushin kuliya manta sabo bayan an kama shi da laifin satar dabbobin da su ka hada da rago da tumaki a daidai lokacin da ake shirin sallah
  • Matashin da kansa ya amsa laifuffukan da ake zargin ya aikata bayan an gurfanar da shi gaban kotu, inda a nan ne alkaliya V.B. William ta yanke masa hukuncin daurin wata uku
  • Amma ta ba shi zabin tara, inda aka bukaci ko dai ya yi zaman gidan gyaran hali da tarbiyya, ko kuma ya biya kudin ragon da tumakin da ya sace ga mai su ya fanshi kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gano halin da miliyoyin dalibai ke ciki bayan an saida makarantu

Ogun - Wata kotu da ke zamanta a Abeokuta ta kama wani matashi mai shekaru 35, Kabiru Lawal da laifin zambar rago da tumaki sannan ya cefanar da su ya kalmashe kudin.

Matashin mazaunin Olomore a garin Abeokuta ya shaidawa kotu cewa da gaske shi ne ya yi dan hali, bayan ya ci amanar mai dabbobin sannan ya kai su kasuwa ya sayar.

Ogun Map
An daure matashin da ya yi zambar dabbobi tun shekarar 2023 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Vanguard News ta wallafa cewa mai shari’a Mrs V.B. William ta yi masa daurin watanni uku-uku na dukkanin laifukan biyu, watau samun dabbobin ba bisa ka’ida ba da sayar da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ba matashin zabin biyan kudi

Mai shari’a V.B. William a yau ta bawa matashin nan da aka tabbata ya sace rago da tumaki ta hanyar zamba zabin ya biya kudinsu ko ya yi zaman gidan yari da dukkanin laifuka biyu da aka kama shi da su.

Kara karanta wannan

NELFUND ta fadi daliban da su ka cancanci lamunin karatu

A zaman kotun na yau Juma’a, mai shari’ar ta ce zai iya lissafa kudin dabbobin sannan ya biya mai dukiyar, ya kuma yi tafiyarsa.

Pulse.ng ta wallafa cewa tun a shekarar 2023 ake zargin Lawal da lallaba mai dabbobin inda ya kwashe tumaki takwas da rago guda da kudinsu ya kai N300,000 bayan ya ce zai sayar masa da su.

Bayan ya karbi dabbobin tare da sayar da su ne sai ya gudu ya bar jihar Ogun baki daya kafin daga bisani a samu nasarar kama shi.

Abuja: Barayin Raguna sun shiga hannu

A baya kun ji cewa wasu barayin raguna sun shiga hannun hukuma su na tsaka da kokarin cefanar da ragunan da su ka sato a gida wani Alhaji a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na zuwa ne kasa da awanni 48 bayan kama wasu barayin shanu sun kai kasuwar dabbobi ta Abaji a babban birnin tarayya Abuja da zummar sayar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.