Har Yanzu Boko Haram Na Rike da Garuruwa, Shehun Borno Ya Faɗi Hanya 1 da Za a Kwato Su

Har Yanzu Boko Haram Na Rike da Garuruwa, Shehun Borno Ya Faɗi Hanya 1 da Za a Kwato Su

  • Shehun Borno ya magantu kan wasu garuruwa a jihar Borno da har yanzu suke ƙarƙashin ikon 'yan ta'addan Boko Haram
  • Basaraken ya mika korafi ga shugaba Bola Tinubu da jami'an tsaro kan buƙatar kwato wuraren domin samun zaman lafiya a Borno
  • Shehun ya mika korafin ne a lokacin da ya kai gaisuwar sallah ga mukaddashin gwamnan jihar Borno, Dakta Umar Kadafur

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Shehun Borno, Abubakar Umar Ibn Garbai Al-Amin El-Kanemi ya ce har yanzu Boko Haram na rike da wasu garuruwa a jihar.

El-Kanemi ya kuma mika korafi ga gwamnatin tarayya kan buƙatar kwato garuruwan domin tabbatar da cikakkiyar zamana lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Shehun Borno
Shehun Borno ya koka kan yadda Boko Haram ke rike da yankuna a jihar har yanzu. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa basaraken ya fadi hanyar da ya kamata abi wajen ganin an kwato garuruwan a wajen 'yan ta'addan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garuruwan da suke hannun Boko Haram

Shehun Borno ya ce kamarar hukumar Gumazala na cikin wuraren da Boko Haram ke cin karensu ba babbaka har yanzu.

Ya kuma bayyana cewa akwai wurare a ƙananan hukumomin Kukawa da Abadam da har yanzu Boko Haram ke rike da iko.

Hanyar kwato garuruwan

A cikin shawarin da mai martaba Shehun Borno ya bayar, ya ce dole abi 'yan ta'addan Boko Haram har maboyarsu a yaƙesu idan ana son cin galaba a kansu.

Ya kara da cewa matukar ba haka aka yi ba to da wahala a iya kwato wuraren daga hannun 'yan ta'addan, rahoton Leadership.

Ya kamata gwamnati ta kara ƙoƙari

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta bayyana matsayarta kan tarar N10 da aka sanya mata kan Aminu Ado

Mai martaba Shehun Borno ya ce gwamantin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta yi kokari wajen yakan yan ta'adda jihar.

Amma duk da haka ya ce akwai bukatar ƙara kokari wajen ganin an kwato garuruwan da Boko Haram ke rike dasu a jihar.

An yi rashi a masarautar Borno

A wani rahoton, kun ji cewa mai martaba Shehun Borno, Abubakar Ibn Garbai El-Kanemi ya tafka babban rashi bayan rasuwar ɗansa a jihar Borno.

An sanar da mutuwar Alhaji Shehu Mustapha El-Kanemi a daren Asabar, 27 ga watan Afrilun shekarar 2024 bayan ya sha fama da jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng