An gano manyan wurare uku da har yanzu ke karkashin Boko Haram a Arewa maso Gabas
- An gano manyan wurare uku da har yanzu ke karkashin Boko Haram a Arewa maso Gabas
- Yankunan sune tafkin Chadi, dajin Sambisa da kuma tsaunikan Mandara, duk a jihar Borno
- Sai dai shugaban sojin Najeriya, Tukur Buratai, ya dauki alkawarin kwato dukkan wuraren da 'yan ta'addan suka kwace
An gano manyan wurare uku a yankin arewa maso gabas a matsayin manyan wuraren da ke karkashin 'yan ta'addan Boko Haram.
Hakan ya biyo bayan mako daya da shugabannin tsaro da wasu masu ruwa da tsaki a yankin suka dauka suna tattaunawa.
Yankunan sune tafkin Chadi, dajin Sambisa da kuma tsaunikan Mandara, duk a jihar Borno, gidan talbijin din Chanels ta ruwaito.
Tattaunawar da aka yi a karkashin ikon shugaba Buhari, ya samu halartar gwamnonin arewa maso gabas.
"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da jama'ar jihar Borno da dukkan yankin arewa maso gabas cewa zai yi duk abinda ya dace wajen tabbatar da ganin ya bada kariya ga rayuka da dukiyoyin jama'ar jihar Borno," Gwamna Babagana Zulum ya sanar da manema labarai a Maiduguri bayan isowarsa daga Abuja a ranar Lahadi.
Ya kara da cewa, "Mun tattauna a kan abubuwan da za su karfafa tsaro a tafkin Chadi da tsaunikan Mandara tare da dajin Sambisa. Kuma ina tunanin tattaunawa da shugaban ma'aikatan tsaro da muka yi zai matukar taimakawa."
KU KARANTA KUMA: Shugabancin kasa a 2023: Matasan Ohanaeze sun bayyana mutum 2 da suka zaba
Gwamnan ya ce Buratai, wanda shine shugaban sojin kasa, ya dauki alkawarin kwato dukkan wuraren da 'yan ta'addan suka kwace.
Ya tabbatar da cewa, sabon tsarin shugaban kasa da shugabannin tsaro zai tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Borno.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng