Kungiyar CODE Ta Fadi Mataki 1 da Tinubu Zai Dauka Domin Magance Matsalar Tsaro

Kungiyar CODE Ta Fadi Mataki 1 da Tinubu Zai Dauka Domin Magance Matsalar Tsaro

  • Wata Kungiya mai zaman kanta (CODE) ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan magance matsalolin tsaron Nijeriya
  • Kungiyar ta ce bayan cika shekaru 25 ana mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya ya kamata a samu cigaba wajen magance matsalolin tsaron kasar
  • Shugaban kungiyar, Mista Hamzat Lawal ne ya bayyana haka yayin wani taro na musamman da kungiyar ta gudanar a birnin tarayya Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Wata kungiya mai zaman kanta (CODE) ta koka kan yadda matsalar tsaro ta zama ruwan dare a Najeriya.

A karkashin haka kungiyar ta bayyana hanya daya da shugaba Bola Tinubu zai bi wajen kawo karshen matsalar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Anambara ya fadi albashin da ya kamata a biya ’yan siyasa a Najeriya

Bola Tinubu
An bukaci Tinubu ya sanya wa'adin magance matsalar tsaro. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar, Mista Hamzat Lawal ne ya bayyana haka a jiya Alhamis a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkawarin da Bola Tinubu ya yiwa Najeriya

Shugaban kungiyar CODE, Hamzat Lawal ya ce Bola Tinubu ya yi alkawarin sanya sharuda da duk wanda ya ba muƙami.

Mista Hamzat Lawal ya kara da cewa shugaban ya yi alkawarin sauke dukkan wanda ya gaza cimma abin da ake bukata ya yi a mukaminsa.

Matakin samar da tsaro a Najeriya

A karkashin alkawarin da shugaban kasar ya yi ne Hamzat Lawal ya ce ya kamata ya ba shugabannin tsaron Najeriya wa'adin magance matsalolin tsaro.

Hamzat ya ce idan wa'adin ya cika, ba su inganta tsaro ba, sai ya saukesu kamar yadda ya yi alkawari a baya.

Legit ta gano cewa Malam Hamzat Lawal ya ce wannar ita ce hanya daya da Bola Tinubu zai bi wajen samar da tsaro a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana yadda Tinubu ya gina Atiku da sauran mutane a siyasa

Shekaru 25 kan tsarin dimokuraɗiyya

Har ila yau Hamzat Lawal ya yi tsokaci kan cikar Najeriya shekaru 25 tana tafiya kan tsarin dimokuraɗiyya.

Ya ce ya kamata a rika waiwaye ana duba irin nasarorin da aka samu da kuma kalubale da ake fuskanta wanda babban kalubale a halin yanzu shi ne rashin tsaro.

Gwamna ya koka kan rashin tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a jihar da yankin Arewacin Najeriya.

Gwamnan ya bayyana cewa ba a sanar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu haƙiƙanin halin da ake ciki dangane da matsalar rashin tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng