Sallah: Kiristoci Sun Ba Musulmai Gudunmawa, Sun Tura Sako ga Sanusi II, Sultan
- Al'ummar Kiristoci a jihar Kaduna sun taya Musulmai share filin idi domin gudanar da sallah a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni
- Kiristocin sun dauki wannan matakin ne domin karin hadin kai da fahimtar juna a karamar hukumar Kajuru da ke jihar
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bikin sallah a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni a fadin duniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan sallah, Kiristoci a jihar Kaduna sun taya Musulmai sharar masallacin idi.
Fasto Yohanna Buru shi ya jagoranci Kiristocin domin taya al'ummar Musulmai aikin domin karin hadin kai.
Sallah ya hada kan Kiristoci da Musulmai
An gudanar da aikin share filin idin ne a karamar hukumar Kajuru da ke jihar wanda ya hada da Fastoci da limamai a yankin a cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bikin sallah da za a gudanar a ranar Lahadi 16 ga watan Yuni.
"Mun zo nan ne domin taya al'ummar Musulmai share filin idi da kawar da duka datti yayin da ake shirye-shireyn bikin sallah."
"Mun dauki matakin ne domin karin hadin kai da fahimtar juna a tsakanin addinan guda biyu."
"Mun godewa Musulman da irin goyon baya da kuma dama da suka bamu domin taya su share filin iddin."
- Fasto Yohanna Buru
Sakon Fasto ga Sultan da Sanusi II
Fasto Buru ya kuma taya Sarkin Musulmi da Sheikh Dahiru Bauchi da Sheikh Ibrahim Zakzaky murnan zagayowar bikin sallah.
Sauran wadanda ya turawa sako sun hada da Sheikh Ahmed Gumi da Sheikh Salihu Mai-Barota da kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
Yayin da yake martani, babban limamin Kajuru, Akilu Mohammed ya nuna farin cikinsa kan wannan taimakon da Kiristocin suka yi.
Ya ce wannan hali ne mai kyau wanda kowa ya kamata ya yi koyi da shi inda ya ce sun shafe shekaru suna wannan hidima.
Matawalle ya raba ragunan sallah a Zamfara
Kun ji cewa karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi abin alheri ana daf da gudanar da bikin sallah babba a fadin duniya.
Bello Matawalle ya raba raguna 4,860 da mukadan kudi har N390m domin gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng