Sallah: Matawalle Ya Gwangwaje Zamfarawa da Raguna, Ya Raba 390m Daf da Layyah

Sallah: Matawalle Ya Gwangwaje Zamfarawa da Raguna, Ya Raba 390m Daf da Layyah

  • Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya raba raguna 4,860 ga al'ummar jihar domin su gudanar da bukukuwan babbar Sallar 2024 cikin walwala
  • Ƙaramin ministan tsaron a gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kuma ware Naira miliyan 390 domin rabawa magoya bayan jam'iyyar APC a jihar
  • Rabon tallafin da tsohon gwamnan ya yi ya haɗa da zaɓo wasu mutum 140 daga ƙananan hukumomi 14 inda aka ba su N100,000 kowanensu domin bikin Sallah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gabanin bikin babbar sallar 2024, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle ya raba raguna 4,860 ga al'ummar jihar.

Ƙaramin ministan ya kuma ware Naira miliyan 390 domin rabawa magoya bayan jam’iyyar APC da masu ƙaramin ƙarfi wanda hakan na daga cikin al’adarsa a lokacin irin waɗannan bukukuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya samo mafita ga gwamnati kan mafi karancin albashi

Matawalle ya raba raguna a Zamfara
Matawalle ya raba N390m domin bikin Sallah a Zamfara Hoto: Dr. Bello Matawalle
Asali: Facebook

Su wa za su amfana da tallafin Matawalle?

Jaridar Tribune ta ce waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da 'yan kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma akwai shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar.

Sauran waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗa da dattawan jam’iyyar, matasa, ƙungiyoyin mata, malamai, marasa galihu, marayu da gajiyayyu da kuma ƴan jam’iyyar APC a faɗin jihar.

Sauran sun kasance tsofaffin masu muƙami a gwamnatin Matawalle da suka haɗa da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman da manyan daraktoci.

Sauran su ne manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman, mambobin hukumomi da sauransu.

Hakazalika, an zaɓo mutane 140 daga ƙananan hukumomi 14 na jihar tare da ba kowannensu N100, 000 domin tallafa musu a yayin bikin Sallah.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau ya cire dokar hana fita da ya sanya, ya fadi dalili

Marafa ya caccaki Matawalle

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu/Shettima 2023 a jihar Zamfara, Kabiru Marafa ya caccaki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Sanata Kabiru Marafa ya caccaki tsohon gwamnan na jihar Zamfara ne kan sukar Dattawan Arewa da ya yi a can kwanakin baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel