Bayan Tsere da EFCC, Tsohon Gwamna a Arewa Zai Mika Kansa Gobe a Abuja

Bayan Tsere da EFCC, Tsohon Gwamna a Arewa Zai Mika Kansa Gobe a Abuja

  • A karbar, tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya a gobe Alhamis a Abuja
  • Yahaya Bello ya samu tabbaci daga alkalin kotun cewa babu wani abin da zai same shi kan tuhumar da ake yi masa
  • Wannan na zuwa ne bayan tsere-tsere da tsohon gwamnan ya rika yi da hukumar EFCC kan zargin wawushe kudin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana sa ran tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello zai gurfana a gaban kotu a gobe Alhamis 13 ga watan Yuni.

Bello zai kawo kansa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bayan tsere-tsere da hukumar EFCC kan zargin badakalar kuɗi.

Kara karanta wannan

Jigon APC, Salihu Lukman ya nakasa jamiyyar bayan ya yi murabus, ya jero dalillai

Yahaya Bello zai gurfana a gaban kotu bayan guje-guje da EFCC
Yahaya Bello zai mika kansa bayan tawaye ga EFCC. Hoto: Yahaya Bello, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Twitter

EFCC: Yahaya Bello zai mika kansa

Lauyan tsohon gwamnan, Abdulwahab Mohammed ya ce Bello ba ya tsoron EFCC amma yana tsoron halin da rayuwarsa za ta kasance a hannunsu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhammad ya ce ana yiwa Bello barazana a lokuta da dama a Abuja shiyasa ya ɓace gaba daya ba a ganinsa, cewar Leadership.

Lauyan ya ce tsohon gwamnan zai je kotu ne domin wanke kansa madadin ofishin hukumar EFCC a Abuja, Daily Trust ta tattaro.

Yahaya Bello ya samu tabbaci daga kotu

Mai Shari'a, Emeka Nwite ya ce hukumar EFCC tana bin doka kuma ba za ta yi wani abu da zai saɓa doka ba.

Ya ce Yahaya Bello ba shi kadai aka fara gayyata ba kan zargin badakala kudi kuma ba zai zama na karshe ba.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito, tsarin sabon Naira da tsohon gwamnan CBN ya yi ba irinsu Buhari ya amince ba

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar EFCC ke zargin tsohon gwamnan da badakalar makudan kuɗi har N90bn lokacin da yake mulkin jihar Kogi.

EFCC ta shirya binciken El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta zabi wasu daga cikin jami'anta domin fara binciken Nasiru El-Rufai.

Hukumar tana zargin tsohon gwamna da badakalar N423bn lokacin da ya ke mulkin jihar daga 2015 zuwa 2023.

Wannan na zuwa ne bayan Majalisar jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken El-Rufai kan wasu zarge-zarge a gwamnatinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel