Bayan Umarnin Kotu Kan Cafke Kwankwaso, EFCC Ta Dauki Mataki Kan El Rufai

Bayan Umarnin Kotu Kan Cafke Kwankwaso, EFCC Ta Dauki Mataki Kan El Rufai

  • Yayin da kotu ta hana EFCC cafke Rabiu Kwankwaso kan zargin badakala, hukumar ta shirya bincikar Nasir El-Rufai
  • Hukumar ta hada jami'anta da za su fara binciken El-Rufai kan zargin badakalar N423bn lokacin da ya ke gwamnan Kaduna
  • Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Majalisar jihar ya fitar da rahoto da ke tabbatar da zargin tsohon gwamnan a Kaduna

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Hukumar EFCC ta zabi wasu daga cikin jami'anta domin binciken tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin binciken N423bn da ake zargin El-Rufai lokacin da ya ke mulkin jihar Kaduna.

EFCC da shirya binciken El-Rufai bayan dakatar da ita kan hukunta Kwankwaso
Hukumar EFCC ta tattara jami'anta da za su binciki Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Facebook

Kaduna: EFCC ta shirya binciken El-Rufai

Kara karanta wannan

Gwamanti ta fadi yadda za ta kwato bashin da ta rabawa mutane a lokacin Corona

The Nation ta tattaro cewa nan ba da jimawa ba hukumar za ta gayyaci El-Rufai domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran wadanda za su amsa tambayoyi a ofishin hukumar sun hada da mukarrabansa da suka rike mukamai daga 2015 zuwa 2023.

Duka manyan mukarrabansa da suka hada da daraktocin hukumar tattara kudin jihar da kwamishinoni za su amsa tambayoyi a cewar Punch.

Za a binciki jami'an gwamnatin El-Rufai

Sai kuma wadanda suka rike mukamin masu binciken kudi na tsawon shekaru takwas amma ban da Amina Ja'afar Ladan wacce Injiniya ce da ta shafe wata daya a ofis.

Hakan bai rasa nasaba da rahoton Majalisar jihar kan zargin badakalar da El-Rufai da mukarransa suka yi.

Kotu ta takawa EFCC birki kan Kwankwaso

Wannan na zuwa ne bayan kotu a jihar Kano ta haramtawa hukumar EFCC cafke Rabiu Kwankwaso kan zargin badakala.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja, an kama miyagu

Kotun ta hana EFCC yunkurin cafkewa da hantara da kuma tuhumar Kwankwaso da wasu mutane guda bakwai kan zargin.

PDP ta tsoma baki kan binciken El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa Jami'yyar PDP a jihar Kaduna ta shawarci Gwamna Uba Sani kan lamarin binciken Nasir El-Rufai.

Jam'iyyar ta bukaci Uba Sani da ya gayyaci hukumomin yaki da cin hanci domin bincikar El-Rufai da hukunta shi.

PDP ta ce wannan binciken ya tabbatar da zargin da ta dade tana yi kan gwamnatin El-Rufai da aka dade ana almundahana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.