Harajin Noma: Ƴan Bindiga Sun Karɓi Naira Miliyan 6.2 Daga Manoman Ƙauyukan Kaduna

Harajin Noma: Ƴan Bindiga Sun Karɓi Naira Miliyan 6.2 Daga Manoman Ƙauyukan Kaduna

  • An ruwaito cewa 'yan bindiga sun karbi Naira miliyan 6.2 da buhu hudu na shinkafa daga hannun manoman wasu kauyukan Kaduna
  • A makonnin baya ne 'yan bindigar suka fatattaki manoman daga gonakinsu tare da ba su umarnin biyan N100,000 kudin harajin noma
  • Wani manomi daga yankin ya ce 'yan bindigar sun karbi kudin tare da buhu hudu na shinkafa hudu kafin su yarda su yi noman

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Rahotanni na nuni da cewa 'yan bindiga sun amince wa manoman karamar hukumar Kachia da ke jihar Kaduna su ci gaba da noman bana.

Manoman Kaduna sun biya 'yan bindiga haraji.
Kaduna: Manoma sun biya 'yan bindiga N6.2m kudin harajin noma. Hoto: The Washington Post / Getty Images
Asali: Getty Images

Wannan na zuwa ne bayan da aka ce 'yan bindigar sun karbi Naira miliyan 6.2 da buhu hudu na shinkafa daga hannun manoman.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun tarwatsa sansanin 'yan ta'adda a Abuja, an kama miyagu

Manoma sun biya 'yan bindiga N6.2m

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun fatattaki manoman Unguwar Jibo da na Nasarawa-Azzara lokacin da suke aikin gonarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce 'yan bindigar sun nemi manoman su hada masu N100,000 duk mutum daya ma damar suna so son yin noma a wannan daminar ta bana.

A makon da ya gabata aka ce manoman sun mika wa 'yan bindigar N725,000 da suka tara, sai dai wannan tayin kudin bai samu karɓuwa ba.

Abin da manoman yankin suka ce

Wani manomi daga yankin, ya shaidawa jaridar cewa manoman sun hada Naira miliyan 6.2 bayan tsawon makonni suna karo-karo.

Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun karbi kudin da kuma buhu hudu na shinkafa a yankin Katari inda suka lamunce masu su ci gaba da noman.

Har yanzu ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur kan wannan rahoto ba.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Tinubu ya yi jawabi ga 'yan Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar da jawabin kai tsaye ga al'ummar Najeriya domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyyar kasar.

Jawabin shugaban ya fi karkata kan tattalin arziki, sabon mafi ƙarancin albashi, tsaro da dai sauran abubuwan da suka shafi gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel