Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga

  • Manoman jihar Zamfara suna shirin ganawa da manyan shugabannin 'yan bindiga da suka addabesu a jihar Zamfara
  • Kungiyar manoman ta bayyana cewa, sasancin ne kadai zai basu tabbatacciyar kariya daga farmakin da ake kai musu a gonakinsu
  • Kamar yadda mai magana da yawun AFAN ya bayyana, manoman sun tafka asara mai tarin yawa ta biliyoyi kan rashin daukin FG

Zamfara - Manoma a jihar Zamfara sun shirya ganawa da shugabannin 'yan bindiga a jihar domin sasantawa kan kariya da barinsu su yi noma a gonakinsu.

Idan za a tuna, manoma da mazauna wasu yankuna a jihohin arewa sun ce suna biyan haraji ga 'yan bindiga domin gujewa farmakinsu, jaridar Punch ta rahoto.

Zamfara Map
Rashin Tsaro: Manoman Zamfara Zasu Yi Zaman Sasanci da 'Yan Bindiga. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Manoman wadanda suka yi magana karkashin inuwar Kungiyar Manoman Najeriya, reshen jihar Zamfara, sun ce zasu gana da 'yan bindigan a yau Asabar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun sako wata tsohuwa mai shekaru 90 da aka sace a jirgin Kaduna

Kakakin AFAN, Abdulhafiz Alkali a ranar Alhamis, ya jajanta yadda gwamnatin tarayya tayi watsi da su da kuma duk wani kokarin samarwa manoma tsaro.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

"Abinda na sani game da tsaron manoma shine sasanci da 'yan ta'adda. A Zamfara nake rayuwa yanzu. Na san cewa akwai taron da za a yi tsananin manoma da 'yan bindiga a ranar Asabar.
"Mun tafka asarori da yawa a jihar Zamfara. Mun aike da wasiku ga gwamnatin tarayya sa su samar mana da tsaro tun shekaru biyar da suka gabata bayan mun yi korafin cewa 'yan bindiga sun saka mu gaba."

Ya kara da cewa:

"Muna bukatar daukin gwamnatin tarayya amma bata taba kawo mana ba. Abubuwan da muka rasa a shekaru shida da suka gabata ya kai N30 biliyan zuwa N50 biliyan.
"Mutane daga kasashe da jihohi daban-daban sukan zo Dansadau siyan kaya a kalla na N50 biliyan a kowacce shekara, amma a yanzu muna samun N2 biliyan zuwa N3 biliyan ne.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka kashe fitaccen lauya a Zamfara

"A jihar Zamfara, muna kasuwancin N200 biliyan zuwa N300 biliyan amma 'yan bindigan sun dakile mana kasuwancin. Mun rubuta wasiku, mun yi korafi amma har yanzu babu martani daga gwamnatin tarayya."

Yan Bindigan da Suka Dauke Fasinjojin Jirgin Kasa na Shirin Aure ‘Yar shekara 21

A wani labari na daban, Tukur Mamu ya bada sanarwar cewa ‘yan bindiga na shirin auren wata daga cikin fasinjojin jirgin da aka sace a hanyar Abuja-Kaduna.

The Cable ta ce Alhaji Tukur Mamu wanda na-kusa ne da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana haka a ranar Juma’a, 19 ga watan Agusta 2022.

Yayin da yake bada sanarwar sakin wasu mutane hudu a jiya, ‘dan jaridar ya fadakar da mutane cewa ‘yar autar da ke tsare ta na fuskantar barazana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel