'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma

'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma

- Harkar tsaro tana kara tabarbarewar a jihar Zamfara

- 'Yan bindiga sun canja salo a kauyukan jihar, musamman ga manoma

- Yanzu suna sanya wa manoma haraji matsawar suna so su yi girbi

Al'amarin 'yan bindiga kullum kara faskara yake yi a jihar Zamfara. Don yanzu haka sun fara sanya wa manoma haraji kafin su yi girbi.

Wani Abdussalam Ibrahim Ahmed ya ce: "Yan bindiga sun umarcemu da mu biya N800,000 matsawar muna son su bar mu mu yi noma cikin kwanciyar hankali, kuma har mun biya."

Kamar yadda yace, sai da suka biya haraji kafin su bar su su yi girbi.

Har yanzu, 'yan ta'adda suna cigaba da kashe-kashe, kai hare-hare, har da yi wa mata fyade a jihar.

A tattaunawar da BBC tayi da mutumin, ya sanar da su yadda manoman kauyaku kamar Duhuwar Saulawa, Duhuwar Maikulungu, Baudi, Zagadi, Doka da Tungar Makeri; aka saka musu haraji yanzu haka yawancinsu sun biya.

Abu mafi takaici shine, yadda bayan manoman sun gama biyansu kudaden, suka jira suka gama girbin tas, sannan suka kwashe buhunhunan kayan amfanin gonar suka tsere, musamman a kauyen Duhuwar Maikulungu.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Kungiya ta bukaci gwamnatin Kano ta kori ma'aikata 'yan Faransa

'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma
'Yan bindiga na sanya mana haraji kafin su bar mu girbin abinda muka noma, Manoma. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP

A wani labari na daban, rundunar sojoji ta kashe wata mata mai dauke da abu mai fashewa da wasu 'yan bindiga 7 a Borno da jihar Yobe, The Punch ta wallafa.

Matar, tayi yunkurin fasa abun a sansanin sojoji na 7 da ke Bama, jihar Borno, a ranar 3 ga watan Nuwamba, amma rundunar suka yi gaggawar kashe ta.

Kamar yadda takardar tazo a ranar Talata, daga mukaddashin darektan kakakin yada labarai, Birgediya janar Bernerd Onyeuko, ya ce rundunar sojin ta sansani na 11 da aka mayar Gamboru, sun samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 2 a maboyarsu da ke kauyen Bulama Lumbe da na Ndufu, wasu kuwa suka tsere da munanan raunuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel