Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Gwamna Ya Take Sultan, Zai Sauya Dokar Masarautu

Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Gwamna Ya Take Sultan, Zai Sauya Dokar Masarautu

  • Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Gwamnatin Sokoto za ta sauya fasalin dokar nadin masu rike da saraurar gargajiya
  • Kwamishinan Shari'a a Sokoto, Nasir Binji shi ya ba da tabbacin ga gwamnatin jihar domin samun ikon nadin hakimai da dagatai
  • Kafin wannan mataki na kwamishinan, Majalisar sarkin Musulmi ne ke da ikon nadin hakimai da dagatai a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Kwamishinan Shari'a a jihar Sokoto, Nasir Binji ya ba gwamnatin jihar damar nadawa da sauke hakimai da dagatai.

Gwamnatin ta samu damar sauya sashe na 76 na dokokin kananan hukumomi da masarautu a jihar.

Gwamna zai sauya dokar masarautu a Sokoto ana tsaka da rigimar na Kano
Gwamna Ahmed Aliyu zai sauya dokar nadin sarauta a jihar Sokoto. Hoto: @ahmedaliyusok.
Asali: Twitter

Sokoto: Gwamna zai sauya dokar masarautu

Kara karanta wannan

'Yan majalisa na neman mayar da ofishin mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya zama 2

Kwamishinan ya bayyyana haka ne ga manema labarai bayan ganawar Majalisar zartarwa a jihar, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin daukar wannan mataki, Majalisar Sarkin Musulmi ne kadai ke da ikon nadin hakimai da dagatai a jihar.

Binji ya ce sabuwar dokar za ta ba Majalisar Sultan damar gabatar da hakimai ko dagatai ne kadai yayin da gwamna ke da ikon naɗa su.

Wannan na zuwa ne bayan korar wasu masu rike da saraurar gargajiya a jihar kan badakalar filaye da zargin hannu a matsalar tsaro.

Hakiman da aka sauke sun hada da na Unguwar Lalle, da Yabo, da Wamakko, sai Tulluwa, Ilela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu da Giyawa.

Za a sauya dokar ƙananan hukumomin Sokoto

Har ila yau, gwamnatin jihar za ta yi gyaran fuska kan dokar ƙananan hukumomi wurin tsawaita wa'adin ciyamomin.

Wa'adin a sabuwar dokar zai kasance shekaru uku ga shugabannin ƙananan hukumomi sabanin shekaru biyu da suke yi.

Kara karanta wannan

Sallah: Bayan Dikko Radda na Katsina, gwamnan Sokoto ya yi abin alkairi ga ma'aikata

Wannan mataki zai lalata dokar tsohuwar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da ta rage wa'adin zuwa shekaru biyu daga uku.

Gwamnan Sokoto ya gwangwaje ma'aikata da albashi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya amince da biyan ma'aikata albashin watan Yuni daga ranar Litinin 10 ga watan Yuni.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne domin ragewa ma'aikata radadi da kuma yin Sallah cikin walwala.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda ya ba ma'aikata kyautar N15,000 da bashin N30,000 domin bukukuwan sallah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel