Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Ƴan Najeriya Hutun Kwana 1

Ranar Dimokuradiyya: Gwamnatin Tarayya Ta Ba Ƴan Najeriya Hutun Kwana 1

  • Ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya ayyana ranar Laraba 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu ga 'yan Najeriya
  • 12 ga watan Yuni na kowace shekara gwamnatin tarayya ta tsayar domin yin bikin murnar zagayowar ranar dimokuradiyyar Najeriya
  • Dakta Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya ayyana ranar hutun a madadin gwamnatin, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yaba kokarin Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar dimokuradiyya ta bana.

Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba a matsayin ranar hutun dimokuradiyya. Hoto: @BTOofficial
Asali: Twitter

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan rana.

Kara karanta wannan

Karin albashi: Fitaccen malamin addini ya fadi abin da 'yan Majalisu ya kamata su dauka

Gwamnati ta ba da hutun dimokradiyya

Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar sakatare a ma’aikatar Dr Aishetu Gogo Ndayako, in ji rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya ce:

“Yayin da muke sake bikin ranar dimokuradiyya a cikin tarihin kasarmu, ina neman ‘yan Najeriya da su tsaya tsayin daka kan tsarin mulkin dimokradiyyar."
"Akwai bukatar mu zurfafa tunani a kan kokarin da 'yan mazan jiya da suka yi wajen tabbatar da cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya."

Gwamnati ta yi kira ga 'yan Najeriya

Jaridar The Punch ta ruwaito Hon. Tunji-Ojo ya sake nanata cewa Shugaba Bola Tinubu ya kuduri aniyar kawo sauyi mai kyau domin farfado da tattalin arziki da inganta tsaro.

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da abokan kasar da su yaba da ci gaban da aka samu, da kuma fatan samun dorewar dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Kotu ta hana gwamnati kama Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jiha da ke da zama a Kano, ta dakatar da hukumar EFCC daga kamawa, tsarewa, hantara, gayyata ko tuhumar Rabiu Musa Kwankwaso.

Kotun ta bayar da wannan umarnin ne a zamanta na jiya Litinin, 10 ga watan Yunin bayan da Kwankwaso, jam'iyyar NNPP da wasu mutane suka shigar da kara gabanta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel