Kano: Bidiyon Kwamandojin Hisbah 44 a Fadar Sarki Sanusi II, Sun Fadi Matsaya

Kano: Bidiyon Kwamandojin Hisbah 44 a Fadar Sarki Sanusi II, Sun Fadi Matsaya

  • Shugabannin Hisbah a kananan hukumomi 44 a Kano sun yi mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar
  • Kwamandojin sun ziyarci sarkin ne a fadarsa jiya Litinin 10 ga watan Yuni domin nuna goyon bayansu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shari'a bayan mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar sarauta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II, Hukumar Hisbah ta ziyarci sarkin a fadarsa.

Shugabannin hukumar a kananan hukumomi 44 da ke jihar Kano sun yi mubaya'a ga Sarki Sanusi II a fadarsa.

Hukumar Hisbah ta ziyarci Sanusi II a Kano
Kwamandojin Hisbah sun kai ziyara fadar Sarki Sanusi II a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Asali: Facebook

Kano: Ziyarar Hisbah fadar Muhammadu Sanusi II

Kara karanta wannan

Sanusi II ya ragargaji Gwamnatin Tarayya bayan dawowa mulki? an gano gaskiya

A cikin faifan bidiyo da Kano Emirate Council ta wallafa a shafin X, an gano kwamandojin suna sarawa Sanusi II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamandojin sun kai ziyarar ne a jiya Litinin 10 ga watan Yuni a fadar sarkin domin nuna goyon bayansu ga Sanusi II.

Daga bisani an gudanar da addu'o'i domin neman taimakon ubangiji kan jagorancin sarkin da ci gaban Kano.

Halin da ake ciki kan shari'ar masarautu

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar jihar a kotu bayan tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Babbar kotun jihar ta yi zama kan shari'ar inda ta sanya Alhamis 13 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraran karar.

Hakan ya biyo bayan maka Gwamna Abba Kabir da Majalisar jihar da Aminu Babba Dan Agundi ya yi kan matakin rushe masarautu a jihar.

Kara karanta wannan

Masarautun Kano: Kotu ta sanya lokacin fara sauraran shari'a, ta fadi ka'idar zama

Kano: Dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado

A wani labarin, kin ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake gudanar da sallar Juma’a a yau 7 ga watan Yuni a jihar.

Dubban jama’a ne suka tarbi sarkin yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma’a duk da shari’ar da ake yi.

Hakan na zuwa yayin da ake ci gaba da shari'a kan masarautun jihar bayan tuge Aminu Ado Bayero daga kujerar sarautar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel