Sanusi II Ya Ragargaji Gwamnatin Tarayya Bayan Dawowa Mulki? an Gano Gaskiya

Sanusi II Ya Ragargaji Gwamnatin Tarayya Bayan Dawowa Mulki? an Gano Gaskiya

  • An yi bincike kan gaskiyar wani faifan bidiyo da ake yadawa cewa Sanusi II ya soki gwamnati bayan dawowa kujerar sarautar Kano
  • A faifan bidiyon an gano Sanusi II yana caccakar Gwamnatin Tarayya tare da cewa babu mai yi musu bazara komai girmansa a kasar
  • Sai dai binciken kwa-kwaf ya tabbatar da cewa bidiyon ya kwana biyu domin an nade shi ne tun a shekarar 2022 a Lagos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - An yi ta yaɗa wani faifan bidiyo inda aka gano Muhammadu Sanusi II na sukar Gwamnatin Tarayya.

A cikin maganganunsa, Sanusi II ya ja hankalin gwamnatin da ta yi kokarin kawo sauyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Sarki Sanusi II ya faɗi abin da zai kawo ci gaba a ƙasa

An gano gaskiya kan bidiyon da Sanusi II ke sukar gwamnati
A shekarar 2022, Sanusi II ya caccaki Gwamnatin Tarayya a Lagos. Hoto: @Opeyemtech.
Asali: Twitter

Bidiyon Sanusi II da ake yaɗawa

Wani mai amfani da kafar X, @Row_Haastrup shi ya wallafa bidiyon inda ya ce Sanusi II ya yi wannan jawabi ne bayan dawowa kujerar sarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kalamai masu tsauri da ratsa zuciya daga Sanusi Lamido Sanusi bayan dawowa kujerar sarautar Kano."

- Cewar mawallafin

Binciken kwa-kwaf kan bidiyon Sanusi II

Sai dai an yi bincike ta amfani da 'Google reverse image' wanda ya tabbatar da cewa bidiyon ya dade tun shekarar 202 aka nade shi..

An gano cewa Sanusi II ya yi wannan jawabi ne tun a watan Agustan shekarar 2022 a Lagos yayin wani babban taro.

Yayin taron a Lagos, Sanusi II ya ce babu wani mai yi musu barazana ko da kuwa gwamna ne ko shugaban kasa.

"Babu wanda zai yi mana barazana ko gwamna ko shugaban kasa da ba za mu fada maka cewa ya yi kuskure ba."

Kara karanta wannan

Kano: Fitaccen basarake ya magantu kan dawo da Sanusi II, ya tura masa sako na musamman

"Mun kama wani layi ne daban, amma da siyasa muka shiga da watakila zan iya zama gwamna ko shugaban kasa."

- Muhammadu Sanusi II

Dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado

Kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake gudanar da sallar Juma’a a ranar 7 ga watan Yuni a jihar.

Dubban jama’a ne suka tarbi sarkin yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma’a duk da shari’ar da ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.