Hajj: Najeriya ta Kammala Jigilar Alhazanta zuwa Kasa mai Tsarki

Hajj: Najeriya ta Kammala Jigilar Alhazanta zuwa Kasa mai Tsarki

  • Hukumar kula da alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala jigilar maniyyatanta zuwa kasar Saudiyya domin sauke farali
  • Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ya isa saudiyya, inda ya bayyana fatan wadanda su ka bi jirgin yawo su iso kan lokaci
  • Malam Jalal Arabi ya kara da cewa suna shirin rage kwanakin da alhazansu su ke yi a kasa mai tsarki bayan sun kammala ibadarsu ta aikin hajji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Saudi Arabia- Hukumar kula da alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa na Shirin rage kwanakin da alhazan Najeriya ke yi a kasa mai tsarki bayan kammala aikin hajji.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Wata Hajiya daga Najeriya ta hallaka kanta a Madina, Saudiyya ta yi martani

Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ne ya bayyana matakin a ranar Litinin jim kadan bayan ya sauka a filin jirgin Prince Mohammed Bin Abdulaziz da ke Madinah.

Hajji
Hukumar alhazai ta ce an kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya Hoto: Haramain
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa shugaban NAHCON ya ce matakin zai taimaka wajen rage gararamba da alhazan Najeriya ke yi idan an kamala aikin hajji duk shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Duk alhazan Najeriya sun sauka Madina,” Arabi

Shugaban hukumar NAHCON ta kasa, Malam Jalal Arabi ya ce an yi nasarar kwashe dukkanin alhazan Najeriya zuwa Madina kai tsaye.

Ya bayyana cewa wannan nasara ce mai kyau, inda ya kara da cewa cikin ikon Allah za a samu sakamakon da ake bukata yayin aikin hajjin bana.

Najeriya ta kafa tarihin jigilar hajji a bana

Malam Jalal Arabi ya kara da cewa wannan ne karon farko cikin lokaci mai tsawo da aka kwashe dukkanin alhazan Najeriya awanni 72 da rufe jigilar alhazan.

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

A yau ne dama hukumar ta NAHCON ta bayyana cewa za ta kammala kwashe maniyyatan aikin hajjin bana kamar yadda aminiya ta wallafa.

Ya bayyana fatan su ma jiragen yawo za su yi nasarar karaso da maniyyatan Najeriya Saudiyya kafin lokacin da aka bayar na daina shiga da alhazan.

Tsananin zafi: Saudiyya ta dauki mataki

A wani labarin kun ji cewa hukumomin Saudiyya sun dauki matakai domin rage rasuwar alhazai saboda tsananin zafi yayin aikin hajji kuma an yi nasara.

Wani bincike da asibitin Sarki Faisal ya yi ya gano cewa matakan da mahukuntan Saudiyya su ke ta dauka shekaru 40 baya sun yi tasiri wajen rage matsalolin zafi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel