Hajjin 2024: An Sanya Ranar Kammala Jigilar Maniyyatan Najeriya Zuwa Saudiyya

Hajjin 2024: An Sanya Ranar Kammala Jigilar Maniyyatan Najeriya Zuwa Saudiyya

  • Maniyyatan jihohin Najeriya da suka rage za su tashi zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da Hajjin bana a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024
  • Hukumar Alhazai ta Najeriya ta tsara cewa jirgin ƙarshe na maniyyata 211 da suka rage zai tashi zuwa birnin Madina a ranar Litinin
  • Hukumar NAHCON ta kuma sanar da cewa za a fara dawo da Alhazan Najeriya daga ƙasa mai tsarki a ranar 22 ga watan Yunin 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jirgin ƙarshe ɗauke da maniyyatan jihohin Najeriya zai tashi a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024 zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta kuma sanar da cewa za a fara jigilar dawo da Alhazan Najeriya daga Saudiyya a ranar 22 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Hajjin 2024: Wata Hajiya daga Najeriya ta rasu a Madina

Za a kammala jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya
Jirgin karshe na maniyyatan Najeriya zai tashi ranar Litinin, 10 ga watan Yuni Hoto: NAHCON
Asali: Twitter

Maniyyata nawa suka rage su tafi hajji?

A yanzu dai akwai sauran maniyyata 211 waɗanda suka fito daga jihohin Bauchi, Kebbi, Neja, Sokoto, Zamfara da kuma Abuja, cewar rahoton jaridar Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maniyyatan za su tashi a jirgin ƙarshe daga Abuja zuwa Madina ne a yayin da ya rage saura kwana uku a fara aikin Hajjin shekarar 1445AH.

Jirgin kamfanin FlyNas na ƙasar Saudiyya shi ne kuma zai kwashe rukunin ƙarshe na jami’an aikin Hajji kamar yadda hukumar NAHCON ta tsara, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Da alama kowa zai samu aikin hajji

Hakan zai kawo ƙarshen jigilar maniyyatan jihohi zuwa ƙasa mai tsarki duk da tsaikon da aka samu sakamakon yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka yi a satin da ya wuce.

Shi ma kamfanin jirgin sama na Aero contractors zai kammala jigilar maniyyatansa na jirgin yawo daga Najeriya a ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

"Kuɗin sun yi yawa" Gwamnoni sun mayar da martani kan sabon mafi ƙarancin albashi

Ana sa ran sauran kamfanonin jiragen yawon za su kammala kwashe maniyyatansu daga Najeriya kafin a rufe filin jirgin sama na biranen Madinah da Jeddah.

Alhazan Najeriya sun isa Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jirgin alhazan farko daga jihar Kebbi ya tashi zuwa ƙasa mai tsarki kamar yadda aka tsara domin sauke faralin aikin hajji a wannan shekara 2024.

An ƙaddamar da fara jigilar Alhazan na Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel