Gwamnatin Kano Ta Harzuƙa Ƴan Jarida, Sun Dauƙi Mataki Kan Abba da Jami’ansa

Gwamnatin Kano Ta Harzuƙa Ƴan Jarida, Sun Dauƙi Mataki Kan Abba da Jami’ansa

  • Biyo bayan taron gaggawa da ta yi a yau Litinin, kungiyar 'yan jaridu masu aiko da rahoto sun janye aiki daga gwamnatin Kano
  • Kungiyar ta haramta wa mambobinta yaɗa duk wani aiki da ya shafi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ma'aikatun jihar baki daya
  • Shugaban ƙungiyar, Aminu Garko ya yi nuni da cewa 'yan jaridunsu na fuskantar barazana da hantara a yayin gudanar da ayyukansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Kungiyar 'yan jaridu masu aiko da rahotanni da ke karkashin kungiyar 'yan jarida ta kasa (NUJ) ta sanar da kauracewa duk wasu ayyukan da suka shafi gwamnatin jihar Kano.

Wannan matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na kungiyar da shugabanta Aminu Ahmed Garko ya jagoranta a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Kaduna, rundunar 'yan sanda ta magantu

Gidan gwamnatin jihar Kano
'Yan jarida sun dakatar da yada rahoton ayyukan gwamnatin Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Kungiyar 'yan jaridu masu kawo rahoton sun yi wannan taron ne saboda cin kashin da ake yi masu a gidan gwamnati da hukumomin gwamnati a jihar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A duk lokacin da mambobinta suka ne dauko rahoto da ya shafi gwamnati da jami'anta, suna fuskantar hantara, a cewar kungiyar.

"Ana cin zarafin 'yan jarida a Kano" - Garko

Shugaban ƙungiyar ya ce:

"Duk da tarin korafe korafe da muka yi da kuma kokarin tattaunawa da gwamnati da jami'anta domin shawo kan matsalar, amma babu wani sauyi da aka samu.
"'Yan kungiyar mu na fuskantar cin fuska, hantara da kyara, wasu lokutan ma bar da cin zarafi yayin gudanar da ayyukan su."

Aminu Garko ya ce abin baƙin ciki ne a ce gwamnatin jihar ta fifita bara gurbin masu kawo rahoto a kan kwararrun 'yan jarida.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Kano: 'Yan jarida sun janye aiki

Kungiyar ta yanke hukunci cewa:

"Dangane da hakan, muna bakin cikin sanar da ku cewa ba za mu sake daukar rahoton duk wani taro, sanarwar gwamnatin jihar ko yin hira da wani jami'in gwamnati ba.
"Za mu zuba idanu mu ga matakin da gwamnatin jihar za ta dauka, idan ta ba mu tabbacin kare martabar ma'aikatanmu, to za mu dawo bakin aiki."

Kungiyar ta yi kira ga dukkanin manema labarai da ke karkashin ta da su yi biyayya ga wannan umarni tare da mara mata baya wajen yaƙi da cin zarafin 'yan jarida a Kano.

Abba ya kaddamar da ginin titunan Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin gina tituna biyu a garuruwan daban daban da za su lakume Naira biliyan 2.6.

Wannan na daga shirin gwamnatin Kano na gina titunan karkara a garuruwa 10 da ke mazabun tarayya uku na jihar in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel