Kano: Dan Majalisar Yanki Ya Yi Wa Marayu 120 Gata, Za Su Fara Zuwa Makaranta
- Akalla marayu 120 ne wani kansila a karamar hukumar Wudil ta jihar Kano, Bashir Aliyu, ya dauki nauyin karatun su
- Kamar yadda ya bayyana yayin kaddamar da rabon kayayyakin karatu ga yaran, Hon Aliyu ya ce tallafin zai gyara goben marayun
- Kansilan ya jaddada cewa zai dauki nauyin karatun wadanda suka ci gajiyar tallafin tun daga karama har zuwa babbar sakandire
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Kansila mai wakiltar gundumar Achika ta karamar hukumar Wudil a jihar Kano, Bashir Aliyu, ya dauki nauyin karatun yara marayu 120 da aka kora daga makaranta.
A wani bikin bayar da kayayyakin karatu ga yaran da aka gudanar a gundumar Achika a ranar Lahadi, Hon. Aliyu ya ce ya yi hakan domin gyara makomar marayun.
Kansila ya dauki nauyin karatun marayu
Hon. Aliyu ya ce za a yi wa yaran rajista a karamar sakandare ta gwamnati da ke Achika da kuma karamar sakandaren Arabiyya ta Achika, in ji rahoton Daily Nigerian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa zai dauki nauyin karatun wadanda suka ci gajiyar tallafin tun daga karama har zuwa babbar sakandire ko da kuwa ba ya rike da wani mukamin siyasa.
Kansilan ya yi nuni da cewa, hakan shi ne irin gudunmawar da zai bayar wajen ci gaban jihar Kano wadda za ta karfafa wa marayu da marasa galihu.
An raba kayan karatu ga daliban
Ya bayyana cewa ya fito da wannan shiri ne a wani yunkuri na tabbatar da makomar yara musamman marayu da a halin yanzu ke samun koma baya wajen yin karatu.
Hon. Aliyu ya bayyana cewa daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin, 65 mata ne yayin da 54 kuma maza ne.
Kayayyakin da aka raba wa wadanda suka ci gajiyar tallafin sun hada da littattafan rubutu guda 1,200, jakunkunan makaranta 120, saiti 240 na kayan makaranta da kuma saiti 240 na takalma.
Abba ya biya wa dalibai kudin NECO
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf ya biya wa dalibai 119,903 kudin jarabawar NECO da NBAIS ta 2024.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince a fitar da Naira biliyan 2.9 domin biyan kudin jarabawar ne ga daliban da suka samu makin 'C' a darusa 5 na jarabawar 'Mock.'
Asali: Legit.ng