Yara 100 A Najeriya Na Mutuwa A Kowace Awa Saboda Tamowa, In Ji UNICEF

Yara 100 A Najeriya Na Mutuwa A Kowace Awa Saboda Tamowa, In Ji UNICEF

  • Asusun Lamunin Kananan Yara Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ta ce yara 100 ke mutuwa kowanne awa a Najeriya saboda tamowa
  • Nemat Hajeebhoy, babban masaniya kan abinci mai gina jiki a UNICEF ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taro a Abuja
  • Ta bayyana cewa rashin samar da abinci masu gini jiki babban barazana ce ga yara a kasar da makomar kasar kasancewarsu manyan gobe

FCT, Abuja - Kowanne awa, kimanin yara 100 yan kasa da shekara biyar suke mutuwa saboda rashin cin abinci masu gina jiki wato tamowa, a cewar Asusun Lamunin Kananan Yara Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF.

Babban masaniyar abinci mai gina jiki na UNICEF, Nemat Hajeebhoy, ta bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja, yayin wani taro da manema labarai da Majalisar Kula Abinci na Kasa da hadin gwiwar ofishin mataimakin shugaban kasa suka shirya, da tallafin UNICEF, Ma'aikatan Lafiya da wasu suka shirya.

Kara karanta wannan

Magidanci ya gamu da fushin alkali yayin da ya daba wa surukinsa kwalba a kai

UNICEF
Yara 100 A Najeriya Na Mutuwa A Kowace Awa Saboda Tamowa, In Ji UNICEF. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Hajeebhoy, rashin cin abinci mai gina ciki barazana ne ga girman yaran Najeriya, The Punch ta rahoto.

UNICEF: Yara 100 ke mutuwa duk awa daya a Najeriya saboda matsananciyar rashin abinci mai gina jiki

Ta ce rashin samun abinci masu gina jiki na shafar lafiyar, cigaban yara kuma yara da yawa ba su samun abinci masu gina jiki da sinadarai da suke bukata don girma.

Ta ce:

"Idan ba su samu kulawa ba, yara da ke da fama matsananciyar rashin abinci mai gina jiki sun fi mutuwa kusan sau 12 fiye da yara masu lafiya.
"Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, UNICEF ta yi kiyasin cewa yara miliyan 14.7 yan kasa da shekaru biyar za su fuskanci matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a wannan shekarar

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan Boko Haram Sun Kai Hari Sansanin Yan Gudun Hijra, Sun Kashe Mutum 4

"Yara miliyan 13 za su yi fama da matsakaicin rashin abinci mai gina jiki sannan kuma yara miliyan 1.7 za su yi fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki."

Ta yi nuni da cewa za a yi asarar kashi 15 cikin dari na GDP na Najeriya idan ba an dauki mataki kan lamarin ba.

Tamowa barazana ce ga makomar yaran Najeriya - Dr Oyeleke

Ta kara da cewa matsalar karancin abinci babban barazana ce ga makomar Najeriya kuma gida daya cikin uku baya iya siyan abinci mai gina jiki mafi sauki.

A bangarensa, shugaban sashin abinci mai gina jiki da tsaron abinci na Ma'aikatar Noma da Cigaban Karkara, Dr Rasaq Oyeleke, ya ce ba za a iya cimma muradin cigaba 17 ba idan ba a inganta tsarin samar da abinci ba.

Kalamansa:

"Ya zama dole tsarin da abinci ya samar da wadataccen kuzari da muhimman sinadarai don ingantaccen lafiyar mutanen kasa."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Soki CBN, Ya Fadi Dalilin Canza N200, N500 da N1000 Daf da Zabe

Jerin Jihohin Biyar 5 Da Yara Ba Su Da Yanci A Najeriya

Asusun lamunin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce kawo yanzu jihohi 5 cikin 31 na Najeriya ba su kafa dokar kare hakkin kananan yara ba.

Kungiyar kare hakkin yara ta kasa da kasa ce ta bayyana hakan a lokacin da ta yabawa gwamnatin jihar Kebbi bisa kafa dokar kare hakkin yara da ta yi kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel