Adabi: An kafa kungiyar marubuta littattafan Hausa a jihar Bauchi

Adabi: An kafa kungiyar marubuta littattafan Hausa a jihar Bauchi

- Jihar Bauchi ta fara gogayya da sauran takwarorinta da ke kokarin ganin sun bunkasa fannin adabin Hausa, ta hanyar kafa kungiyar BAHWA

- Hajiya Hafsat Azare ta samu nasarar lashe zaben kujerar shugabar ƙungiyar, yayin da Sani Hamza Funtua ya zama Sakatare

- Tun farko, marubutan jihar sun tuntubi jiga-jigan mutane masu kishi da son daukaka adabi don daga darajar harshen Hausa a jihar

A ranar Asabar 6 ga watan Yuli, jihar Bauchi ta fara gogayya da sauran takwarorinta da ke kokarin ganin sun bunkasa fannin adabin Hausa, ta hanyar kafa kungiyoyin marubuta, inda marubutan adabin Hausa yan asalin jihar suka assasa (kafa) kungiyar marubuta littattafai a harshen Hausa ta din-din-din.

Gamayyar marubutan jihar da ke rubutu da babban yaren cikin gida Najeriya, sun yi taron zaman tattaunawa a birnin Bauchi kan samar da sabuwar ƙungiyar marubutan Hausa ta Jihar a karon farko a tarihi.

A zaman da ya faru, marubutan sun cimma nasarori da dama; na lankayawa kungiyar suna da wanzar da tasirin ta bayan tattara bayanai da shawarwari daga bakin Manazarta kuma Marubuta da babban lauyansu, inda a karshe suka sanyawa kungiyar sun suna 'Bauchi Hausa Writers Association (BAHWA).

KARANTA WANNAN: Safiya Badamasi: A karo na farko, musulma bahaushiya ta samu matsayin SAN

Adabi: An kafa kungiyar marubuta littattafan Hausa a jihar Bauchi
Adabi: An kafa kungiyar marubuta littattafan Hausa a jihar Bauchi
Asali: Original

Bayan zabarwa kungiyar wannan suna, sai kuma zaben shuwagabannin rukon kwarya a manyan kujeru biyar ya biyo baya, inda Hajiy Hafsat Umar Ɗan Tanko Azare ta samu nasarar lashe zaben kujerar shugabar ƙungiyar.

Daga cikin manyan mukaman, wakilin Legit TV Hausa, Malam Sani Hamza Funtua ya samu nasarar zamowa Sakataren kungiyar, yayin da Sakina Salis Imam ta zamo ma'aji, Aminullah Mohammad Elder ya zamo jami'in kula da walwala, da kuma Musaddam Faridat Musa Sweery a matsayin jami'ar hulda da jama'a.

Hajiya Hafsat Azare, shugabar kungiyar BAHWA
Hajiya Hafsat Azare, shugabar kungiyar BAHWA
Asali: Original

A jawabinta, shugabar kungiyar, Hajiya Hafsat Azare, ta bayyana dalilan da suka sa har aka kirkiri kungiyar da suka hada, bunkasa adabin Hausa a jihar, tallafawa marubuta littattafan Hausa musamman wadanda ke tasowa, wallafa littattafai da za su kawo canji a cikin al'umma, samar da gidauniya karkashin kungiyar da za ta rinka tallafawa marayu da marasa galihu da dai sauransu.

Tun kafin zaman kago kungiyar, marubutan cikinta sun samu damar tuntubar wasu jiga-jigan mutane masu kishi da son daukaka Adabi a jihar, da nufin neman shawarwari daga garesu da kuma basu matsayin iyayen kungiya domin kare martaba da mutuncinta a jihar da ma fadin kasar baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng