Marayu: Gwamnan Arewa Ya Raba Tallafin N50,000 Ga Kowane Mutum 1, Ya Jawo Ayar Alƙur'ani

Marayu: Gwamnan Arewa Ya Raba Tallafin N50,000 Ga Kowane Mutum 1, Ya Jawo Ayar Alƙur'ani

  • Gwamna Mai Mala Buni na Yobe ya kaddamar da rabon tallafin tsabar kuɗi N50,000 ga marayu aƙalla 1,000 a watan azumin Ramadan
  • Wannan ba shi ne karo na farko ba domin gwamnan ya maida shirin tallafin marayu a matsayin wani aiki da gwamnatin ke yi duk shekara
  • Mala Buni ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ci gaba da bayar da sadaƙa ga mabukata da marasa galihu har bayan watan azumi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Kowane mutum ɗaya daga cikin marayu 1,000 da aka zaɓo daga dukkan sassan jihar Yobe ya samu tallafin N50,000.

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ba marayu 1,000 tallafin N50,000 a wani ɓangare na inganta rayuwa da jin daɗi a tsakanin marayun jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta faɗi gaskiya kan biyan kuɗin fansa yayin ceto ɗaliban Kaduna

Gwamna Mai Mala Buni.
Gwamnatin Buni ya waiwayi marayu yayin da ake tunkarar Sallah Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Mala Buni ya kaddamar da fara rabon tallafin kuɗin ga marayu a ɗakin taro da ke gidan gwamnati a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ya yi a wurin taron, Gwamna Buni ya ce gwamnatinsa ta ƙirƙiro shirin bai wa marayu tallafin kuɗi ne domin kyautata rayuwarsu da jin daɗinsu.

Buni ya jawo aya a Alƙur'ani

Ya kuma jawo aya a cikin Alƙur'ani mai girma wanda ta kwaɗaitar da masu imani buƙatar tausaya wa marayu da kuma mabuƙata.

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da wannan aiki, inda ya bukaci sauran masu hannu da shuni da su yi koyi da abin da gwamnati ke yi ga marayu.

"Ina yaba wa ɗaidaikun mutane da kungiyoyi wadanda a cikin wannan wata na Ramadan suke raba abinci kyauta ba mabukata da sauran marasa galihu kamar yadda gwamnati ke yi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan ceto daliban da aka sace a Kaduna, ya sha sabon alwashi

"Ya kamata mu ƙara dagewa kuma mu ci gaba da ba da sadaƙa har bayan watan Ramadan. Muhimmancin irin wannan karimcin shi ne yana ƙara mutunta juna, ƙauna kuma a wannan yanayin yana kawar da ƙiyayya da hassada.
"Fiye da wannan, irin waɗannan ayyukan suna kawo yardar Allah da ni'ima ga ɗaiɗaikunmu da al'umma baki ɗaya tare da jawo mana ɗumbin nasarori a rayuwa."

- Mai Mala Buni.

Gwamnan ya maida shirin tallafawa marayu a matsayin wani aiki na shekara-shekara, inda a 2022 ya raba N50,000 ga marayu 200 da aka zaɓo daga dukkan ƙananan hukumomin Yobe, rahoton Independent.

Fatima Maina, wata ƴar asalin jihar Yobe ta tabbatar mana da lamarin, inda ta ce ƙanwarta na cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin marayun Gwamna Mala Buni.

Amma ta shaidawa Legit Hausa cewa ba ta tabbacin ko marayun da aka ba tallafin sun kai mutum 1,000 ko ba su kai ba.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa sanatoci a wurin buɗa bakin azumin watan Ramadan a Villa

"Wannan abu ne mai kyau a musulunci, kanwata na cikin waɗanda suka amfana kuma a zahirin gaskiya mun ji daɗi," in ji ta.

Ramadan: Gaskiyar kuɗin ciyarwa a Kano

A wani rahoton kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Ysusuf ya bayyana gaskiyar kudin da ya ware don ciyar da al'ummar jihar a cikin watan Ramadana

Ya kuma shawarci 'yan jarida da su daina yada labaran da basu tabbatar ba, inda ya bayyana bacin ransa kan hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel