Albashin Shugaban kasa, Ministoci da ‘Yan Majalisa Shekaru 45 da Suka Wuce a Najeriya
Abuja - A yanzu kusan babu labarin da ake yi irin mafi karancin albashin da ya kamata a biya ma’aikaci a Najeriya a kowane wata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
An shafe wata da watanni ana wannan tattaunawa a sakamakon cire tallafin fetur da kuma tashin kudin wutar lantarki da aka yi.
Legit Hausa ta shiga littatafan tarihi, ta lalubo albashin da aka fara biyan shugabannin Najeriya lokacin da ake jamhuriyya ta biyu.
Wata tsohuwar jaridar Daily Times da aka buga a farkon Nuwamban 1979 ta nuna albashin shugaban kasa, ministoci da ‘yan majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Albashin shugabannin Najeriya a 1979
1. Shugaban kasa
Marigayi Shehu Usman Aliyu Shagari ya rika tashi da N50, 000 a kowane wata a matsayinsa na shugaban kasa mai cikakken iko.
2. Mataimakin Shugaban kasa
Gwamnatin tarayya ta biya Dr. Alex Ekwume N30, 000 a duk wata lokacin da yake mataimakin Shugaban kasar Najeriya a 1979.
3. Shugaban majalisar dattawa
A lokacin da Joseph Wayas yake shugaban majalisar dattawa, albashinsa a wata daga gwamnati shi ne N22, 000 kusan $14 a yau.
4. Shugaban majalisar wakilai
Shugaban majalisar wakilai, Hon. Edwin Ume-Ezeoke ya karbi 40% na albashin shugaban kasa a lokacin yana ofis a 1979.
5. Albashin manyan ministocin 1979
Manyan ministocin gwamnatin tarayya da ake da su suna da N16, 000. Idan za a tuna a wancan lokaci an hada-kai da jam’iyyar hamayya.
Albashin sauran manyan jami’an gwamnati
6. Sakataren gwamnatin tarayya - N16, 000
7. Masu ba shugaban kasa shawara - N16, 000
8. Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya - N16, 000
9. Mataimakin shugaban majalisar dattawa - N18, 000
10. Mataimakin shugaban majalisar wakilai – N17, 000
11. Kananan Ministoci – N14, 000
12. Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa - N18, 500
13. Sanatoci - N17, 000
1979: Albashin sauran 'yan majalisa
14. Yan majalisar wakilai - N16, 000
15. Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai – N17, 500
16. Shugabannin kwamiti a majalisar dattawa – N17, 000
17. Shugaban kwamiti a majalisar wakilai – N16, 500
18. Shugabanni a majalisar wakilai – N17, 000
Tattalin arziki a mulkin shugaba Tinubu
Ku na da labari cewa an fahimci tattalin arzikin Najeriya a karkashin Bola Tinubu bai fi lokacin da Muhammadu Buhari yake mulki ba.
Bayan tsadar abinci, farashin fetur ya tashi daga kimanin N200 zuwa N800 a dalilin janye tallafin fetur da aka yi a karshen Mayun 2023.
Asali: Legit.ng