Manyan Ayyukan da Aka Bukaci Bola Tinubu Ya Karasa a Jihohin Arewa

Manyan Ayyukan da Aka Bukaci Bola Tinubu Ya Karasa a Jihohin Arewa

  • Wata Kungiya a Arewa ta yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu kan ya karasa ayyukan raya a kasa a Arewa
  • Kungiyar ta yi kiran ne yayin da take taya shugaban kasar da sauran jami'an gwamnati murnar cika shekara daya a kan karaga
  • Daraktan kungiyar, Hamisu Isa ya lissafa ayyuka da aka fara da dama a Arewa waɗanda suna bukatar kulawar gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Arewa - Wata kungiya mai zaman kanta a yankin Arewa ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan karasa ayyukan da aka fara Arewa.

Kungiyar ta bukaci yan majalisun tarayya da su saka baki wajen ganin ayyukan da aka fara a yanki sun kammala.

Kara karanta wannan

Karin albashi: Rundunar 'yan sanda ta fitar da bayanin da zai hana 'yan kwadago yajin aiki

Shugaba Tinubu
Kungiya ta bukaci Bola Tinubu ya karasa ayyuka a Arewa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta ce karasa ayyukan za su kawo cigaban yankin da ma masa baki daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da aka nemi Tinubu ya karasa

1. Aikin wutar Mambila

Kungiyar ta ce kusan shekaru 40 kenan da fara maganar wutar Mambila amma har yau ba a kammala ba.

Ta ce idan shugaban kasar ya kammala aikin wutar za a samu damar magance matsalolin tattalin arziki da suka addabi Najeriya.

2. Hako danyen mai a Kolmani

Har ila yau kungiyar ta koka kan yadda aka ji shiru kan fara gabatar da harkokin kasuwanci a rijiyar mai da aka tona a Kolmani.

A lokacin mulkin Muhammadu Buhari ne aka fara tonon man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi.

3. Titin jirgin Kano zuwa Maraɗi

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bijiro da bukata domin hana kungiyar kwadago tsunduma yajin aiki

Kungiyar ta yi kira na musamman ga shugaban kasa kan karasa titin dogon Kano-Kaduna-Maraɗi.

Ta kuma kara da cewa titin dogon da ya hada Kano da Dutse ba riga an fara shi ba duk da cewa yana hade da aikin.

Sauran ayyukan da ke jiran Tinubu

Sauran ayyuka sun hada da hanyoyi da dama a yankin, dasa bututun iskar gas daga Abuja zuwa Kano (AKK), kammala kamfanin Ajakuta da dai sauransu.

Daraktan bincike na kungiyar, Hamisu Isa Sharifai da jami'in yada labaran kungiyar, Mahmoud Adnan Audi ne suka yi kiran.

An koka kan tsadar tumatur

A wani rahoton, kun ji cewa masu noman tumatur a jihar Bauchi sun koka kan yadda karin kudin mai ya hana manoma da dama nomar rani a jihar.

Manoman sun ce tsadar man fetur da karin kudin wuta sun yi tasiri sosai kan dakile ayyukan nomar rani wanda hakan ya jawo tashin farashin kayan gwari a Najeriya baki daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng