Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Kaduna, Sun Cafke Masu Ba Su Bayanai

Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Jihar Kaduna, Sun Cafke Masu Ba Su Bayanai

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a jihar Kaduna sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda shida a wani samame
  • Sojojin na rundunar 'Operation Whirl Punch' sun kashe ƴan ta'addan ne a ƙauyen Galadimawa da ke cikin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar wanda ya ba da sanarwar ya kuma bayyana cewa sojojin sun cafke wasu mutum.uku masu ba ƴan ta'addan bayanai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar ‘Operation Whirl Punch’ sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda shida a jihar Kaduna.

Sojojin sun kuma cafke wasu mutum uku da ake zargi da haɗa baki da ƴan ta'addan a wani samame na musamman a ƙaramar hukumar Giwa.

Kara karanta wannan

"Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 624, sun ceto mutum 563 da aka sace", DHQ

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Kaduna
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a jihar Kaduna Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samuel Aruwan ya bayyana cewa rundunar sojojin ce ta bayyana hakan ga gwamnatin jihar yayin da take bayani kan ayyukanta a jihar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar

Kaduna: Yadda sojoji suka hallaka ƴan ta'adda

Ya bayyana cewa dakarun sojojin bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta'adda a yankin, sun gudanar da aikin sintiri a Galadima cikin ƙaramar hukumar Giwa.

"Dakarun sojojin sun fara yada zango a ƙauyen Sabon Sara, inda suka fahimci cewa ƴan ta'adda sun tsere sun bar garken shanun da suka sato."
"Sojojin sun ƙwato shanun sannan suka miƙa su ga hannun mutanen ƙauyen kafin su ƙara gaba. Daga nan sai suka hango ƴan ta'addan a kasuwar Galadimawa."

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki sojoji a shingen bincike

"Nan da nan aka yi musayar wutar da ta jawo sojojin suka hallaka ƴan ta'adda shida."
"Bayan gudanar da bincike a kasuwar, sojojin sun cafke masu haɗa baki da ƴan ta'addan da masu ba su bayanai. An kuma ƙwato babura guda biyu da wayoyin hannu guda huɗu."

- Samuel Aruwan

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda 624 a cikin watan Mayun 2024.

Sojojin sun kuma cafke ƴan ta'adda 1,051 tare da masu ba su bayanai yayin da suka ƙwato man fetur na sata wanda kuɗinsa ya kai miliyoyin Naira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel