"Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 624, Sun Ceto Mutum 563 da Aka Sace", DHQ

"Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 624, Sun Ceto Mutum 563 da Aka Sace", DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi bayani kan ayyukan dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da zaman lafiya a wurare daban-daban na ƙasar nan
  • DHQ ta bayyana cewa a cikin watan Mayun 2024, sojoji sun hallaka ƴan ta'adda mutum 624 tare da ceto wasu mutum 563 da aka yi garkuwa da su
  • Daraktan yaɗa labarai na DHQ wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya kuma ƙara da cewa an cafke ƴan ta'adda mutum 1,051 ciki har da masu ba su bayanai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewan dakarun sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta'adda 624 a cikin watan Mayun 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na bayar da tallafin N250,000 ga 'yan Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Dakarun sojojin sun kuma cafke ƴan ta'adda 1,051 da suka haɗa da masu ba su bayanai yayin da suka ceto mutum 563 da aka yi garkuwa da su.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 624
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 624 a watan Mayu Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Edward Buba ya kuma gargaɗi fararen hula kan takalar faɗa da hallaka jami'an tsaro na sojoji.

Wace nasara sojoji suka samu kan ƴan ta'adda?

Daraktan yaɗa labaran ya kuma bayyana cewa dakarun sojoji a cikin watan na Mayu, sun ƙwato makamai 707, alburusai 16,487 da ɗanyen man fetur da aka sace wanda kuɗinsa ya kai N705,836,036.00.

Ya bayyana cewa makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigu ƙirar AK-47 guda 411, bindigu ƙirar gida guda 234, manyan bindigu guda 43, ƙananan bindigu guda 231, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai farmaki cikin kasuwa a Kaduna, an rasa rayukan bayin Allah

Sauran sun haɗa da alburusai na musamman masu kaurin 7.62mm guda 10,782, alburusai guda 4,310 na NATO masu kaurin 7.62mm, alburusai guda 1,623 masu kaurin 7.62 x 54mm.

Sauran kayayyakin da sojojin suka ƙwato sun haɗa da litar ɗanyen man fetur da aka sace guda 4,871,470, litar tataccen man fetur na sata guda 931,416 da sauran kayayyaki.

Ƴan bindiga sun hallaka sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki dakarun sojojin Najeriya a wani shingen bincike a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun hallaka sojoji uku tare da ƙona motar sintirin jami'an tsaron kafin daga bisani suka ƙona shingen binciken da sojojin suke gudanar da aikinsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel