Dausayin Ramadan: Samun kuzari da karsashi game da Sallar Dare, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadan: Samun kuzari da karsashi game da Sallar Dare, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

Akwai wasu ladubba da ake so mutum ya kula da su waɗanda za su ƙara masa karsashi da nishadi idan yana son ya yi ƙiyamul laili. Su ne kamar haka:

1. Mutum ya shirya cewa shi yana son ya yi tsayuwar dare ne ta hanyar yin bacci ɗan kaɗan irin wanda ake yi da rana wanda ake cewa ƙailula ta yadda zai rage masa nauyin bacci da daddare, sannan ya daina zaman hira har dare ya tsala, ko kalle-kallen talabijin, ko ɗanne-ɗannen wayar hannu, wanda wannan zai iya sawa jiki ya yi nauyi idan an zo an kwanta ba za a iya tashi ba.

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya zai kawo karshen yan bindiga a Najeriya, Gwamnan dake son gaje Buhari ya gano

2. Mutum ya yi niyyar yana so ya tashi ya yi sallar dare don neman kusanci ga Allah ﷻ domin hadisi ya zo daga Abud Darda'i daga Ma’aiki ﷺ inda yake cewa,”Wanda ya zo shimfiɗarsa ya kwanta a zuciyarsa, yana so ya tashi ya yi nafilfili da daddare sai idonsa ya rinjaye shi bai farka ba har ya wayi gari, to za a rubuta masa abin da ya yi niyya, wannan baccin kuma zai zama sadaƙa a gare shi.” (128)

3. Mutum ya yi bacci da alwala domin yin bacci da alwala yakan hana mutum ya yi bacci mai nauyi ƙwarai.

4. Mutum ya yi bacci a kan ɓangarensa na dama, saboda hadisin Ummina Hafsat inda take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya zo kwanciya yakan sanya hannunsa na dama a ƙarƙashin kumatunsa na dama.” (129) 5. Idan mutum ya ji tsoron ba zai farka da daddare ba, to sai ya fara yin wutiri kafin ya kwanta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda 'Yan Bindiga Suka Ci Karen Su Ba Babbaka, Suka Halaka Ma'aikacin INEC a Wurin Aikin Rijistar Zaɓe

6. Mutum ya ambaci Allah ﷻ idan zai kwanta bacci, saboda shi ambaton Allah ﷻ idan za a yi bacci yakan tsare mutum daga sharrin Sheɗan, kamar yadda nana A’isha ta tuwaito cewa, idan Ma’aiki ﷺ ya zo makwancinsa a kowane dare yakan haɗa hannayensa guda biyu sai ya tofa ƙulhuwallahu da falaƙi da naasi a cikinsu sai ya shashshafe iya inda hannunsa zai kai, kuma yana farawa daga kansa da fuskarsa sannan gaban jikinsa, yana yin haka sau uku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

7. Idan mutum ya tashi daga bacci ya goggege alamar kwantsa a idanunsa da fuskarsa ko yawun bacci idan ya zuba, sannan ya ambaci Allah ﷻ ya yi alwala, kamar yadda ya zo a cikin hadisin Bukhari da Muslim.

8. Mutum ya yi amfani da aswaki, saboda hadisin Huzaifatu Bn Yaman da yake cewa, idan Ma’aiki ﷺ ya tashi da daddare zai yi tahajjudi yakan fara goge bakinsa da askwaki. (131)

Kara karanta wannan

Idan ban gyara Najeriya a shekara ɗaya ba ku mun kiranye, Ɗan takarar shugaban ƙasa ya roki dama a 2023

9. Mutum ya fara buɗe ƙiyamullailinsa da raka’o’i biyu gajeru kafin ya shiga dogaye, kamar yadda Ummina A’ishah ta ke cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance idan zai yi sallar dare yakan farawa da gajerun raka'o'I guda biyu kafin dogaye. Imamu Ahmad da imamu Muslim ne suka rawaito shi.

10. Mutum ya buɗe sallar dare da irin addu'o'in da Ma’aiki ﷺ ya koyar bayan ya yi kabbara, kamar yadda ya zo a hadisi,

11. Mutum ya tsawaita raka'o'in tsayuwar dare, sai dai kada ya yi abin da zai takurawa kansa har ya rasa nishaɗinsa da samun ɗanɗanon ganawa da wanda yake yin sallar dan shi. (133)

12. Mutum zai iya yin sallar nafila a tsaye, kuma zai iya yi a zaune idan ya gaji domin Ma’aiki ﷺ ya yi sallar dare kashi uku:

Ya yi sallah a tsaye gaba ɗayanta daga farko har ƙarshe. ➢

Kara karanta wannan

Dausayin Ramadana: Abubuwa 17 da suka hallata ga mai azumi, Sheikh Aminu Daurawa

Ya yi sallah a zaune daga farko har ƙarshe, wato ya yi ruku'u a zaune. ➢

Ya yi sallah rabi a zaune, rabi kuma a tsaye, wato ya fara sallar a zaune sai ya rage wasu ayoyi kaɗan kamar aya (30) zuwa (40) sai ya miƙe ya ƙarasa sallar a tsaye.

Sannan kuma idan mutum yana sallah sai ya gaji ko ya fara jin bacci, to ya kwanta ya ɗan rintsa domin baccin ya tafi, shi kuma ya sami nutsuwar da zai iya ci gaba da sallar, saboda hadisin da Ma’aiki ﷺ ya shigo masallaci sai ya samu an ɗaura igiya daga wannan al'amudin zuwa wancan, sai ya ce menene wannan? Sai aka ce igiyar zainab ce da take yin sallah idan ta gaji sai ta jingina da ita, sai Ma’aiki ﷺ ya ce, “Ku kwance ta, sannan ya ce, mutum ya riƙa yin sallah da nishaɗinsa shi ya fi idan ya ji kasala ko gajiya sai ya kwanta ya yi bacci. Imamul Bukhari da Muslim suka rawaito shi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Na maida mutum 2,000 sun zama Attajirai a jihata, Gwamnan Arewa dake son gaje Buhari

13. Mutum ya yi karatun Al-ƙur'ani ya rera shi da kyakykyawar murya kuma ya yi shi da bin ƙa'idojin karatu, saboda ayar Al-Ƙur'ani tana cewa, “ka karanta Alƙur'ani ka rangaɗa shi rangaɗawa mai ban sha'awa.” kamar yadda ya zo a cikin suratul muzzammil.

14. Mutum ya riƙa bin ma'anonin fassarar Al-ƙur'ani a ya yin karanta shi, ya kuma riƙa yin ƙoƙari wajen halarto abin da Al-ƙur'ani yake faɗa na umarni ko hani domin samun damar yin kuka a inda ya kamata a yi kukan, ko nuna tsoro domin firgici da tsoro a inda ya kamata aji tsoron, ko nishaɗantuwa a inda nishaɗin ya zo a cikinsa. Saboda hadisin Huzaifah da yace, Ma’aiki ﷺ yana yin karatu ne daki-daki, idan ya wuce wata aya wadda akwai tasbihi a cikinta sai ya tsaya ya yi tasbihin, idan kuma ya wuce ayar da ake neman tsari a cikinta, sai ya tsaya ya nemi tsarin Allah ﷻ a wurin, idan kuma ya wuce ta ayar da take akwai roƙo a cikinta, sai ya tsaya ya yi roƙon.

Kara karanta wannan

Bayan ganawa da Buhari, Sabon shugaban APC ya faɗi hanyar da zasu fitar da magajin Buhari a 2023

15. Mutum ya yawaita addu'a a lokacin karatun Al-ƙur'anin da lokacin sahur da ƙarshen dare a cikin sallah da wajen sallah, saboda hadisin Jabir Bn Abdullahi da ya ce, a cikin dare akwai wata sa'a mutum ba zai dace da wannan sa'ar yana roƙon Allah ﷻ wani abu na alkhairin duniya ko na lahira ba, face sai Allah ﷻ ya ba shi abin, wannan kuma yana faruwa ne a kowane dare.”

16. An so mutum ya tashi iyalansa su yi tare, kamar yadda hadisi ya zo cewa, “Wanda ya tashi iyalinsa suka yi sallah a cikin dare za a rubuta shi a cikin masu yin zikirin Allah ﷻ. ya yawa.

17. Mutum ya zama cikin masu yawaita zikirin Allah kuma ya ɗan kwanta ya huta bayan ya gama ƙiyamullaili ko sallar dare kafin alfijir ya fito.

18. Ba a son wanda ya saba yin sallar dare kuma ya dena, saboda hadisin Abdullahi Ɗan Amru ya ce, Ma’aikin Allah ﷺ ya ce da shi, “Ya kai Abdullahi kada ka zama kamar wane mana, ya kasance da dare yana yin tsayuwar dare kuma daga baya sai ya dena.” Kamar Muslim . yadda ya zo a ruwayar Bukhari.

ZA mu ci gaba insha Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel