Sayyada Aisha: Muhimman abubuwa 7 game da matar ma'aiki

Sayyada Aisha: Muhimman abubuwa 7 game da matar ma'aiki

Ana kiranta da diya mai gaskiya kuma abar gasgatawa. Kyakyawa ce ta ajin farko kuma ta auri manzo Allah SAW a shekarun karshe na rayuwarshi.

Idan har za a kira sunan Sayyada Aisha, za a danganta shi da ilimi, soyayya, yarda da hakuri. Ta bada gudumuwa a samuwar sama da hadisai 2,000 a duniya, kuma tana daga cikin wadanda tarihin musulunci ba zai cika ba idan ba a lissafo dasu ba.

Matar Annabi, Khadijatu ce ta goyi bayanshi a lokacin da take a raye kuma Annabi yana birnin Makkah. Aisha kuwa ta taka rawar gani ne a lokacin da Annabi yayi hijirah zuwa garin Madina.

Ga wasu abubuwan mamaki game da Sayyada Aisha.

Daga wajen Allah ne hadin aurensu.

Ka aureta, tunda matarka ce,” cewar mala’ika Jibril a yayin da yake sanar da Annabi a Madina. Annabi ya ga Aisha a mafarki. Mahaifinta yayi matukar farin ciki da wannan hadin daga Allah. Aisha ce mace daya tak da Annabi ya aura budurwa.

Ta taimaka wajen ba wa mata damar zaben miji da kansu

A lokacin jahiliyyah, ba a ba mata damar zaben mazan da zasu aura. A wancan lokacin kuwa wata budurwa ta garzaya gaban Sayyada Aisha da koken cewa za a mata auren dole. Daga nan ne ta kaita gaban Annabi inda ya yi kira ga iyayen da su dena auren dole ga ‘ya’yansu.

DUBA WANNAN: Zargin kisan kai a Kano: Kotu ta ba dan bautar kasa masauki a gidan gyaran hali

Ita ce ayar Allah ta wanke ta a kan mummunan zargin Zina da aka yi mata

A wancan lokacin, Allah ne ya saukar da aya don wanketa a kan mummunan zargin Zina da aka yi mata yayin da aka barta a sansanin yaki.

Tana zama a sahun gaba a yaki

Idan zamu tuna tarihi, Aisha ta kasance jaruma mai zama a sahun gaba a wasu yaki na musulunci da aka yi. Ta halarci yakin Uhud, Khandaq, Banu Qurayza, Banu Mustaliq da Hudaybiya.

Malama ce ga manyan malaman musulunci

A sakamakon kusancinta ga ma’aikin Allah, malamai a wannan lokacin kan garzaya wajen Aisha a kan lamurran addini da suka shige musu. Ta kasance mai tambayar Annabi kusan komai da ya shige mata duhu.

Masoyiya ta hakika ce

Sakamakon kwarewarta da iya soyayya, yasa Aisha ta zama mafi soyuwa ga Annabi. Ta iya soyayya, kauna da kuma nuna kulawa ga Annabi. Wannan soyayyar kuwa ta bayyana har a kwanakin karshen Annabi, don kuwa a kirjinta ya rasu kuma yawunta ne na karshe da ya shiga cikin Annabi.

Ta ga mu’ujizoji masu tarin yawa kuma ta ga mala’ika Jibril

Aisha ta ga mala’ika Jibril a siffar mutane har sau biyu kuma sunyi musayar sallama

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel