Masarauta: 'Yan Sanda Sun Goyi Bayan Gwamnan Kano, An Gargadi Masu Shirin Rigima
- Rundunar yan sandan Kano ta gargadi masu yunkurin tayar da hankali cewa a shirye suke domin daukar matakin da ya dace na wanzar da zaman lafiya a jihar
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya ce an jibge jami’an tsaro a sassan Kano domin dakile yunkurin bata gari
- Wannan mataki ya biyo bayan daukar matakin haramta gudanar da zanga-zanga a Kano da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi a kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa an kara yawan jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci domin dakile duk wani yunkurin rikici.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Kano ta haramta zanga-zanga ko wane iri yayin da ake ci gaba da dambarwar masarauta a jihar.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na facebook, kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce jami’ansu ba za su yi lako-lako da duk wanda aka kama na yunkurin tayar da hankali ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an tsaro sun shirya a Kano
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana kammala shirin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar yayin da ake ci gaba da rikicin masarauta a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya jaddada haramcin gudanar da zanga-zanga, kamar yadda The Nation ta wallafa.
“Jami’anmu dauke da kayan aiki na sassan jihar domin dakile duk wani abu da ka iya tasowa,” a cewar kwamishinan.
Ya kuma shawarci al'umma su ci gaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali domin jami’an tsaro sun shirya tsaf domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
An hana zanga-zanga a Kano
A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin Kano ta sanya dokar hana zanga-zanga domin dakile yunkurin masu kokarin tayar da hankulan mutanen jihar.
Wannan na zuwa ne bayan jan daga da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi na kin amincewa da tube shi da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi a makon da ya gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng