Kungiyar Sarakuna Ta Ba Sanusi II Shawara Kan Rikicin Masarautar Kano

Kungiyar Sarakuna Ta Ba Sanusi II Shawara Kan Rikicin Masarautar Kano

  • Wata ƙungiyar Sarakunan Najeriya ta shawarci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II da ya fice daga fadar Sarkin Kano
  • Ƙungiyar ta buƙaci Sarkin na Kano da ya mutunta doka ta hanyar bin umarnin da kotu ta bayar na fitar da shi daga fadar Sarkin
  • Ta shawarci da ya rungumi ƙaddara sannan ya tuna cewa Allah ne kaɗai ke bayarwa da karɓe mulki a duk lokacin da ya so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata ƙungiyar Sarakunan Najeriya ta shawarci Muhammadu Sanusi II da ya mutunta umarnin babbar kotun tarayya tare da ficewa daga fadar Sarkin Kano cikin gaggawa.

Ƙungiyar ta ce hukuncin da kotun ta yanke a ranar Talata, ya kasance na ƙarshe, inda ta ƙara da cewa ya zama wajibi a ba da fifiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rushe masarautu: Kungiya ta mika kokon bara ga majalisar dokokin Kano

An ba Sanusi II shawara kan ficewa daga fada
Kungiyar sarakuna ta bukaci Sanusi II ya fice daga fada Hoto: @Abdullahiabba_, @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Kano: An buƙaci Sanusi II ya bar fada

Hakan na ƙunshe ne a cikin cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar, Cif Ameh Adaji, da babban sakataren ƙungiyar, Cif Danladi Etsu suka sanyawa hannu a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ta bayyana cewa Sarki ba zai iya yin sarauta ba tare da goyon bayan jama’a ba, kuma zama cikin fada ba bisa ƙa’ida ba abu ne da ba za a amince da shi ba a ko ina a duniya.

Ƙungigar ta ce yin amfani da jami'an tsaro domin fitar da Sanusi II daga fada shi ne mataki na ƙarshe, inda ta buƙace shi da ya guji duk wani abu da zai iya sanyawa a kunyata shi, kawo tashin hankali ko haifar da rikici.

Wace shawara aka ba Muhammadu Sanusi II?

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

Ƙungiyar Sarakunan ta kuma yi kira ga Sanusi II da ya mutunta doka a matsayinsa na tsohon Sarki ta hanyar ficewa daga fadar, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Cigaba da zaman da yake yi a cikin fada duk da umarnin kotu, ba kawai yin karan tsaye ba ne ga doka, har da ɓata sunan masarautar Kano."
"A matsayinsa na Musulmi, ya kamata Sanusi II ya sani cewa Allah ne kaɗai yake ba da mulki kuma yake karɓewa. Ya yi zamaninsa a matsayin Sarki saboda haka ya kamata ya daina ƙoƙarin komawa cikin fada ta bayan fage."

An hana fitar da Sanusi II daga fada

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun jihar Kano ta hana jami'an tsaro na ƴan sanda, DSS da sojoji fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano.

Kotun ta kuma hana jami'an tsaro na ƴan sanda, sojoji da DSS daga gayyata, kamu, muzgunawa ko kawo cikas kan ayyukan Sarkin Kano na 16.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel