Rigimar Masarautar Kano: Abba Ya Ba Jami’an Tsaro Sabon Umarni Kan Masu Zanga Zanga

Rigimar Masarautar Kano: Abba Ya Ba Jami’an Tsaro Sabon Umarni Kan Masu Zanga Zanga

  • Gwamnatin jihar Kano ta haramta duk wani taron jama da ka iya kai wa ga zanga-zanga a fadin jihar
  • Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya ba jami'an tsaro umarnin kama duk wani da aka samu yana zanga-zanga a titunan jihar
  • Gwamnatin ta yi zargin cewa 'yan jam'iyyar adawa sun dauki nauyin dalibai da kungiyoyi domin tada tarzoma kan rusa masarautu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahoton da muka samu yanzu na nuni da cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf ya haramta duk wata zanga-zanga a jihar.

Gwamnan ya kuma ya sanya takunkumi mai tsauri kan duk wani taron jama'a wanda ka iya kai ga yin zanga-zanga a cikin jihar.

Kara karanta wannan

Rushe masarautu: Gwamnatin Kano ta sanya sabuwar doka kan masu zanga zanga

Gwamnatin Kano ta dauki mataki kan masu zanga-zanga
Gwamnatin Kano ta haramta taron jama'a da yin zanga-zanga. Hoto: @Kyusufabba, @masarautarkano
Asali: Facebook

Gwamnan ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Sanusi Bature ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya ba jami'an tsaro umarni

“Bisa ga karfin ikon kujerarsa, gwamnan ya umurci ‘yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC da su kama, tsare da kuma gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano."

- In ji sanarwar Sanusi Bature.

A cewar Bature, gwamnan ya dauki wannan matakin domin dakile duk wani abu da zai iya haifar da karya doka da oda wanda "makiyan jihar ke shiryawa".

"Yan adawa ke shirya zanga-zanga" - Abba

“Mun samu sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin mutane da kungiyoyi domin gudanar da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta daura damarar yakar yan ta'adda, ta ba jami'an tsaro tallafi

Mun gano za a yi amfani da dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa domin tada hargitsi da sunan cewa suna adawa da tsige Sarkin Kano, Aminu Bayero."

Sanusi Bature ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta fito karara ta haramta zanga-zanga, ko taron jama'a ko wane iri ne, kuma za a kama wadanda aka samu sun bijirewa umarnin.

Sanusi II: Lauyoyi sun ba Abba wa'adi

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu lauyoyi sun ba gwamnan Kano, Abba Yusuf wa'adin awa 48 ya tsige Muhammadu Sanusi II daga kujerar Sarkin Kano.

Lauyoyin da suka bayyana kansu da 'kungiyar lauyoyin Arewa' sun yi barazanar daukar matakin shari'a idan gwamnan ya gaza cika sharadin su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel