Siyasar 2027: Tsohon 'Dan Majalisa Ya Hango Makomar Hadakar Atiku da Obi

Siyasar 2027: Tsohon 'Dan Majalisa Ya Hango Makomar Hadakar Atiku da Obi

  • Tsohon 'dan majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Yusuf ya bayyana cewa akwai matukar wahala Atiku Abubakar da Peter Obi su zauna cikin inuwa guda
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da tsofaffin 'yan takarar biyu ke ta tattaunawa domin hadakar da za ta taimaka wajen kwace ikon mulkin kasar nan daga jam'iyyar APC
  • Tsohon dan majalisar ya kara da cewa duk da Peter Obi ya taba yiwa Atiku Abubakar mataimakin shugaban kasa a takararsu ta 2019, zai yi wahala a sake irin wannan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Yusuf ya ce abu ne mai matukar wahala Atiku Abubakar da Peter Obi su hade guri guda domin tunkarar zaben 2027.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Tsohon dan majalisar na wannan batu ne yayin da ake ganin tsofaffin 'yan takarar na bayyana cewa za su cure guri guda domin yin galaba a kan APC a kakar zabe mai zuwa.

Atiku Abubakar
Tsohon dan majalisa ya ce zai yi wuya Atiku Abubakar da Peter Obi su hade Hoto: Atiku Abubakar/ Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce bai ga dalilin rashin hada kai da takwaransa na LP, Peter Obi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Martanin Atiku za a duba,' Yusuf

Tsohon dan majalisar wakilai, Tajuddeen Yusuf ya ce kalaman Atiku Abubakar na nuni da cewa akwai matsala a kokarin hadewa da Peter Obi.

Atiku Abubakar kwanaki kadan bayan tattaunawarsu da Obi ya ce zai ci gaba da tsayawa takara matukar yana numfashi.

Vanguard News ta ruwaito wakilan Peter Obi na cewa ubangidansu ba shi da niyyar hadakar da ke neman kwace karfin ikon mulki kawai.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

A cewar Tajuddeen Yusuf, duk da Peter Obi ya yiwa Atiku Abubakar mataimaki a zaben 2019, hakan zai yi matukar wahala a nan gaba.

'Jam'iyyun adawa na shirin doke APC,' Obi

A baya mun baku labarin cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya ce da gaske suke shirin doke APC a kakar zabe mai zuwa.

A karin bayani da ya yi kan hadakarsu da Atiku Abubakar, Obi ya ce matuƙar da gaske aka kuma aka samu fahimtar juna, zai bayar da hadin kai dari bisa dari.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel