Sarki Na 15 Aminu Ado Bayero Ya Fito Daga Fadar Sarkin Kano, Bidiyo Ya Bayyana

Sarki Na 15 Aminu Ado Bayero Ya Fito Daga Fadar Sarkin Kano, Bidiyo Ya Bayyana

  • Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 ya fito daga karamar fadar da ke Nassarawa da yammacin ranar Litinin, 27 ga watan Mayu
  • Tun ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu aka fara taƙaddama kan sarautar Kano bayan Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa Muhammadu Sanusi II
  • Sai dai har yanzun mutane na son sanin wanene sarki yayin da Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama a ƙaramar fadar sarkin Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan kujerar sarauta, Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano na 15 ya fito daga ƙaramar fadar sarki da ke Nassarawa.

A wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, Aminu Ado ya fito daga fadar ne a kan doki kuma nan take magoya bayansa suka fara murna da kai gaisuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Aminu Ado Bayero.
Sarki na 15 Aminu Ado Bayero ya baro karamar fadar Nassarawa Hoto: Imran Muhammad
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Leadership ta kawo a rahotonta, magoya bayan Aminu Ado Bayero sun ɓarke da shewa tare da miƙa gaisuwa yayin da basaraken ya riƙa amsawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har kawo yanzu babu tabbacin ko Aminu Bayero ya baro fadar ne gaba ɗaya ko kuwa ya ɗan fito ne da nufin zai sake komawa.

Gwamnan Kano, Abba ya maido Sanusi II

Legit Hausa ta tattaro muku cewa a ranar Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan karaga.

Gwamnan ya miƙa wa sarkin takardar shaidar kama aiki a wani taro da aka shirya a fadar gwamnati da ke cikin birnin Kano.

Tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na yanzu, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsige Sanusi daga kujerar sarauta a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kamar Sanusi II, shi ma Aminu Bayero ya yi zaman fada a Nassarawa

Sai dai dawo da Sanusi II da Gwamna Abba ya yi ya zo da tangarɗa bayan Aminu Ado Bayero ya ci gaba da zama a karamar fadar sarki.

Gwamnan Kano ya ba da umarnin a kama Aminu Ado, amma jami'an tsaro suka ce ba za su bi umarni ba saboda kotu ta hana naɗin Sanusi II.

Gwamna Abba ya roƙi Tinubu alfarma

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf Kabir Yusuf ta bukaci Bola Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar Kano

Mataimakin gwamnan jihar wanda ya yi wannan kiran ya buƙaci Tinubu da ya taimaka ya fitar da Aminu Ado Bayero daga Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel