Sarkin Kano: Jerin Hakimai 40 da Suka Yi Mubayi’a ga Sanusi II, 25 Sun Yi Jinkiri

Sarkin Kano: Jerin Hakimai 40 da Suka Yi Mubayi’a ga Sanusi II, 25 Sun Yi Jinkiri

  • Muhammadu Sanusi II ya shiga rana ta uku a gidan masarautar Kano a matsayin sabon Sarki bayan gwamnatin Kano ta yi masa nadi
  • Gwamna Abba Yusuf ne ya rattaba hannu kan dokar da ta rusa masarautu biyar na jihar Kano tare da kuma dawo da Sanusi II kan mulki
  • Ya zuwa yanzu, akalla hakiman Kano 40 cikin 60 ne suka yi mubayi'a ga sabon sarki, Sanusi II, watakila 25 sun yi jinkirin yin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Har yanzu ana ci gaba da tataunawa kan batun rusa masarautun Kano, tsige sarakuna biyar da kuma dawo da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarki.

Kara karanta wannan

Kwana 2 da karbar mulki, Sarki Sanusi II ya nada sabuwar 'Jakadiyar Sarkin Kano'

Kamar yadda al'adar sarauta ta gargajiya ta gada, dole ne hakimai, masu rike da sarautun gargajiya su yi mubayi'a ga sabon sarki, ko kuma su juya baya.

Hakimai sun yi mubayi'a ga sabon Sarkin Kano
Hakimai 40 cikin 65 sun yi mubayi'a ga sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Hoto: @masarautarkano
Asali: Twitter

Ya zuwa yanzu dai, akalla hakiman Kano 40 cikin 60 ne suka yi mubayi'a ga sabon sarki, Sanusi II, kamar yadda shafin masarautar Kano ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin Kano: Hakimai 40 sun yi mubayi'a

Ga cikakken jerin sunayen hakiman Kano da suka yi mubayi'a ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa yanzu.

1. Wazirin Kano

2. Madakin Kano

3. Walin Kano

4. Makaman Kano

5. Sarkin D/Mai Tuta

6. Sarkin Ban Kano

7. Turakin Kano

8. Sarkin Shanun Kano

9. Danburam Kano

10. Dan Isan Kano

11. Dan Lawan Kano

12. Dan Amardin Kano

13. Magajin Garin Kano

14. Dan Majen Kano

Kara karanta wannan

Sanusi II ya bayyana rawar da Tinubu ya taka wajen dawo da shi kan sarautar Kano

15. Dan Kaden Kano

16. Matawallen Kano

17. Sarkin Fulanin Jaidanawa

18. Magajin Malam

19. Dokajin Kano

20. Dandarman Kano

21. Marafan Kano

22. Dallatun Kano

23. Magajin Rafın Kano

24. Sarkin Fadar Kano

25. Bunun Kano

26. Bauran Kano

27. Dan Madamin Kano

28. Dan Galadiman Kano

29. Talban Kano

30. San Turakin Kano

31. Dangoriban Kano

32. Dan Maliki

33. Falakin Kano

34. Yariman Kano

35. Barayan Kano

36. Zannan Kano

37. 'Yan Dakan Kano

38. Fagacin Kano

39. Dan Masanin Kano

40. Wakilin Barden Kano

Sarki Sanusi II ya zabi 'Jakadiyar Sarki'

A jiya Lahadi muka ruwaito cewa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya Ai'in Jafaru Fagge a matsayin 'Jakadiyar Sarkin Kano'.

An ce wannan ne nadin farko da mai martaba Sanusi II ya yi a cikin hadiman fada tun bayan shigarsa gidan sarautar a ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel