InnalilLahi: Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Lamorde Ya Rasu Yana da Shekaru 61
- An shiga jimami bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde a Masar bayan fama da jinya mai tsayi
- Marigayin kafin rasuwarsa ya rike shugabancin hukumar EFCC a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
- Daga bisani Muhammadu Buhari ya sallame shi bayan ɗarewa karagar mulki a watan Nuwambar 2015 da maye gurbinsa da Ibrahim Magu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 61.
Marigayin ya rasu ne a kasar Masar yayin da ya je domin yin jinya kamar yadda aka sanar da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Mayu.
Lokacin da Lamorde ya rike shugabancin EFCC
Premium Times ta tattaro cewa kafin rasuwar Lamorde, ya rike shugabancin hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamorde ya rasu da misalin karfe 3:00 na dare bayan an yi masa tiyata kwanaki uku da suka wuce.
An haifi Lamorde a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 1962 a jihar Adamawa inda ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1986.
An nada Lamorde a matsayin shugaban rikon kwarya na hukumar a watan Nuwambar 2011 a mulkin Goodluck Jonathan, cewar TheCable.
Lamorde ya zama shugaban hukumar EFCC
Daga bisani an tabbatar da Lamorde a matsayin shugaban hukumar a watan Faburairun 2012 har zuwa 9 ga watan Nuwambar 2015.
Bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zabe a 2015, ya cire Lamorde tare da sauya shi da Ibrahim Magu a matsayin shugaban rikon kwarya na hukumar.
Tun farko, an nada Lamorde daraktan ɓangaren ayyuka na EFCC lokacin da aka kirkiri hukumar a shekarar 2003.
Kanin Uba Sani ya rasu a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya sanar da rasuwar kaninsa a ranar Juma'a 24 ga watan Mayu.
Uba Sani ya nuna alhini rasuwar Mukhtar Lawal Isma'il wanda ya kwatanta a matsayin mutun mai ƙan-ƙan da kai da kuma himma a ayyukansa.
A karshe, ya yi addu'ar samun rahama ga marigayin da kuma hakurin jure rashin da suka yi a matsayin ƴan uwansa da masoyansa.
Asali: Legit.ng