Ana Zargin Shi Ya Shirya Komai, Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Tsige Sarakunan Kano

Ana Zargin Shi Ya Shirya Komai, Kwankwaso Ya Yi Magana Kan Tsige Sarakunan Kano

  • Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ba hannunsa a shirin rushe masarautun Kano biyar da Abdullahi Ganduje ya ƙirƙiro
  • Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duk abubuwan da ke faruwa ba ya cikin jihar Kano amma yana dab da komawa kuma zai nemi ƙarin bayani
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da tsige sarakuna biyar tare da naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano ɗaya tilo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta cewa yana da hannu a rushe masarautun jihar.

Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a 2023 ya ce babu ruwansa a matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na tsige sarakunan Kano.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Kwankwaso da gwamnan Kano.
Kwankwaso ya musanta hannu a rushe masarautun Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan kuma jagoran NNPP mai mulkin Kano ya faɗi haka ne yayin wata hira da BBC Hausa a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige sarakuna biyar da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya naɗa bayan rattaɓa hannu kan dokar da majalisa ta yi.

Dokar dai ta rushe dukkan maarautun Kano guda biyar tare da sauke sarakunan da ke kan mulki, kana ta bai wa gwamna damar naɗa sabon sarki guda ɗaya tilo.

Bayan haka ne Gwamna Abba ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano bayan wata ganawa da masu naɗin sarki.

Kwankwaso ya sa aka tsige Sarakunan Kano?

Da yake musanta raɗe-radin cewa shi ya sa aka tsige sarakunan, Kwankwaso ya ce ba ya cikin Kano a lokacin da waɗannan abubuwa ke faruwa.

Kara karanta wannan

Alkalin da ya yi ƙoƙarin hana naɗin Sanusi II ya jawo wa kansa, gwamna ya ɗauki mataki

"Ina nan a Abuja, yadda kuka ga ni nima haka na gani, amma zan yi magana da gwamna da ƴan majalisar domin na samu ƙarin bayani kan yadda lamarin yake," in ji shi

Kwankwaso ya kuma ƙara da cewa ranar Jumu'a watau yau yake sa ran zai shiga Kano kuma zai tuntuɓi gwamnati domin a masa bayani game da wannan lamari.

Sanusi II ya zama sarkin Kano

A wani rahoton, Muhammadu Sanusi II ya koma kan kujerar Sarkin Kano karo na biyu a hukumance yau Jumu'a, 24 ga watan Mayu, 2024.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa Sanusi takardar shaidar naɗa shi sarkin Kano a wani taro da aka shirya a gidan gwamnatin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel