Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Sanusi II Bayan Abba Ya Mayar da Shi Sarkin Kano

Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Sanusi II Bayan Abba Ya Mayar da Shi Sarkin Kano

A ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, 2024 Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammad Sanusi III kan kujerar sarautar Kano bayan shekaru huɗu da tsige shi.

Idan zaku iya tunawa a 2020, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sarki Sanusi II kuma ya maye gurbinsa da Alhaji Aminu Ado Bayero.

Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya dawo kujerar sarauta Hoto: @babarh
Asali: Twitter

Kamar yadda Tribune ta rahoto, matakin Abdullahi Ganduje na sauya Sarkin Kano ya ta da ƙura amma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya bayyana lamarin a matsayin kaddara.

Sai dai a wani sabon lamari da ba a yi mamaki ba, Muhammad Sanusi II ya koma kan karagar Sarkin Kano bayan shekaru huɗu.

Legit Hausa ta tattaro maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Sarkin Kano na 14 a tarihi.

Kara karanta wannan

"Ina godiya Abba": Sarki Sanusi II ya magantu bayan dawowa kujerarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwa 7 game da Sarki Sanusi II

1. An haifi Muhammad Sanusi II a gidan sarauta na fulanin Sullubawa ranar 31 ga watan Yui, 1961.

2. Mahaifinsa, Aminu Sanusi, basarake ne kuma jami'in diflomasiyya, mahaifiyarsa kuma sunanta Saudatu Hussain.

3. Sanusi ya yi karatun firamare a makarantar St. Anne da ke jihar Kaduna kafin daga bisani ya wuce makarantar King’s College a jihar Legas.

Bayan gama sakandire, Sanusi ya shiga jami'ar Ahmadu Bello Zariya inda ya karɓi shaidar digiri na farko a 1981 da digiri na biyu a 1983 duk a fannin ilimin tattalin arziki.

4. Sanusi, wanda ya fara aikin banki a 1985 a Icon Limited, ya rike mukamin gwamnan babban banki CBN daga ranar 3 ga watan Yuni, 2009 zuwa ranar 20 ga Fabrairu, 2014.

5. Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya naɗa Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Ado Bayero, wanda ya ɗauki gomman shekarau a karagar saurauta.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II ya zama sabon sarkin Kano a hukumance, bidiyo ya fito

Muhammadu Sanusi II ya gaji Ado Bayero a kujerar sarautar Kano ranar 8 ga watan Yuni, 2014.

6. A ranar 9 ga watan Maris, 2020, tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje ya sauke Sanusi daga matsayin Sarkin Kano.

7. A halin yanzu, Gwamnan Kano mai ci, Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 kamar yadda aka sani a a baya.

Kotu ta hana mayar da Sanusi II

Rahoto ya zo cewa babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin hana gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar rushe majalisar masarautar Kano.

Mai shari’a Mohammed Liman ne ya yanke hukuncin a kan bukatar da wani basarake, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel