Bidiyon Lokacin da Ganguje Yake Shaguɓe ga Muhammadu Sanusi II Bayan Tube Shi

Bidiyon Lokacin da Ganguje Yake Shaguɓe ga Muhammadu Sanusi II Bayan Tube Shi

  • Yayin da aka rushe masarautun Kano, an gano wani tsohon bidiyo da ake shagube ga Khalifa Muhammadu Sanusi II
  • Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje shi ne ke yin dariya a cikin faifan bidiyon bayan tube Sanusi a 2020
  • Wannan na zuwa ne bayan sake mayar da Muhammad Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano da Abba Yusuf ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An bankado wani tsohon bidiyo da tsohon gwamnan Kano ya ke shagube ga Muhammad Sanusi II.

Hakan ya biyo bayan rushe masarautun Kano guda biyar a yau Alhamis 23 ga watan Mayu 2023.

Ganduje ya taba Muhammadu Sanusi II a wani tsohon faifan bidiyo
An gano wani tsohon faifan bidiyo da Abdullahi Ganduje ke shagube ga Muhammadu Sanusi II bayan tumbuke shi a sarauta. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Ganduje ya yi amfani da dabarar Jonathan

Kara karanta wannan

Abba ya tabbatar da korar Aminu Ado Bayero, ya sanya hannu a dokar da ta rusa su

A cikin faifan bidiyon, Ganduje ya bayyana yadda ya tube Sanusi daga kujerar sarauta ta hanyar amfani da dabarar Jonathan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na jam'iyyar APC ya ce ya yi amfani da maganin Jonathan kan Sanusi domin kawo gyara a masarautar Kano.

Wani mai amfani da kafar sadarwa ta X, @emmaikumeh shi ya yada faifan bidiyon da Ganduje ke cin mutunci ga Sanusi.

Abin da Ganduje ke cewa a bidiyo

"Lokacin da na zama gwamna, a nan ne za ku yi dariya, na ce eh maganin Jonathan."
"Magani ne mai kyau, duk da ni ba likita ba ne, amma zai yi amfani a kan cutar da kuma shi marar lafiyan."
"Na yi amfani da dabarar maganin Jonathan na yi amfani da shi domin kare masarautu kuma na yi amfani da shi yadda ya dace."

Kara karanta wannan

Dawo-Dawo: An sanar da sabon Sarkin Kano, Sanusi II ya zama sarki a karo na biyu

- Abdullahi Ganduje

Har ila yau, Gwamna Abba Kabir ya dawo da Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano bayan rusa masarautun jihar guda biyar da Majalisar dokoki ta yi a yau Alhamis 23 ga watan Mayu.

Majalisar Kano ta rushe masarautun jihar 5

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Kano, ta rusa masarautun jihar guda biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Majalisar ta dauki matakin ne a yau Alhamis 23 ga watan Mayu inda ta bukaci Gwamna Abba Kabir ya sanya hannu.

Daga bisani Abba ya sanya hannu a dokar da ta tabbatar da korar Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna daga sarautar jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel