Gwamnati Ta Fadi Makudan Kudin da Za a Kashe Domin Farfado da Kamfanin Ajaokuta

Gwamnati Ta Fadi Makudan Kudin da Za a Kashe Domin Farfado da Kamfanin Ajaokuta

  • Ministan karafa, Shuaibu Audu ya bayyana ce gwamnatin tarayya na bukatar akalla N35bn domin farfado da kamfanin Ajaokuta
  • Mista Audu ya bayyana haka a wajen taron manema labarai kan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a shekara daya a Abuja
  • Idan har aka farfado da kamfanin, ministan ya ba da tabbacin cewa kamfanin zai rika samar da akalla tan 400,000 na rodi a shekara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Najeriya na ci gaba da tara sama da Naira biliyan 35 da ake bukata domin sake farfado da wani sashe na kamfanin karafa na Ajaokuta.

Ministan karafa, Shuaibu Audu ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai kan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a shekara daya, a ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

29 ga Mayu: Ministoci na cikin matsala, Tinubu ya basu umarni kan ayyukansu

Gwamnatin tarayya ya yi magana kan farfado da kamfanin Ajaokuta
Gwamnatin tarayya za ta karbi N35bn domin farfado da kamfanin Ajaokuta. Hoto: @HonShuaibuAudu
Asali: Twitter

"Gwamnati za ta tara N35bn" - Minista

Jaridar Premium Times ta ruwaito Mista Audu ya ce an ba Tinubu izinin tara Naira biliya 35 da ake bukata daga wata cibiyar hada-hadar kudi ta cikin gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan kuwa na daga wani bangare na kudirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

"Na wasika kuma na mika dukkanin takardun da suka dace ga ministan kudi domin samun damar karbar kudaden a madadin gwamnatin tarayya."

- Shuaibu Audu.

Aikin da kamfanin Ajaokuta zai yi a shekara

Ministan ya ce sashen LSM na kamfanin Ajaokuta da ake kokarin farfadowa ya na da karfin samar da tan 400,000 na rodi a duk shekara, kuma zai taimaka wajen bunkasa masana’antu a Najeriya.

A cewarsa, yana aiki kafada da kafada da ministan ayyuka domin samar da rodin da ake bukata domin ayyukan gina tituna a fadin kasar, in ji rahoton NAN.

Kara karanta wannan

"Yadda Tinubu ya bi ya hana tattalin arzikin Najeriya durkushewa", Kashim Shettima

"Mun fahimci cewa ma'aikatar ayyuka tana buƙatar kimanin tan miliyan bakwai na rodi a cikin shekaru huɗu domin gina waɗannan tituna, kamfanin Ajaokuta na iya samar da tan 400,000 kowace shekara."

- Shuaibu Audu.

Tinubu ya gana da Alhaji Dantata

A wani labarin, mun ruwaito Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rusuna yayin gaishe da Alhaji Aminu Dantata, hamshakin attajirin dan kasuwa kuma kawun Aliko Dangote.

Wannan ce haduwar Tinubu da Alhaji Dantata ta farko a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja tun bayan rantsar da shugaban kasar a 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.