Tinubu Ya Saka Labule da Aminu Dantata, Fitaccen 'Dan Kasuwar Arewa a Abuja

Tinubu Ya Saka Labule da Aminu Dantata, Fitaccen 'Dan Kasuwar Arewa a Abuja

  • Hamshakin dan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Dantata ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Alhaji Aminu Dantata wanda kuma kawu ne ga hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote, ya gana da Tinubu a ranar Talata
  • Wannan shi ne karon farko da Shugaba Bola Tinubu ya gana da dattijon tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An hango Shugaba Bola Tinubu yana gaisawa da babban hamshakin dan kasuwan Kano, Alhaji Aminu Dantata yayin da ya karbe shi a Aso Rock.

Tinubu ya gana da Dantata a Abuja
Tinubu ya nuna girmamawa ga Alhaji Aminu Dantata a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Aminu Dantata ya ziyarci shugaba Tinubu

Shugaban kasar ya karbi bakuncin hamshakin dan kasuwan Kano kuma kawun hamshakin attajirin Afrika, Aliko Dangote a ranar Talata, 21 ga Mayu, 2024, a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Fitattun 'yan Arewa guda 5 da Bola Tinubu ya ba manyan mukamai a jami'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba Tinubu shawara na musamman kan bayanai da tsare-tsare ya wallafa a shafinsa na X.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna girmamawa ga Alhaji Aminu Alhassan Dantata, shugaban rukunin kamfanonin Dantata, lokacin da Dantata ya ziyarce shi a Abuja ranar Talata.
"Dantata, wanda ya cika shekaru 93 a ranar 19 ga Mayu, shi ne jagoran zuriyar gidan Alhassan Dantata a Kano."

- Bayo Onanuga.

Alakar Shugaban kasa Tinubu da Dantata

Wannan shi ne karon farko da shugaban Najeriyan ya gana da dattijon tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Shugaban rukunin kamfanoni na Dantata ya halarci bikin rantsar da Tinubu tare da Dangote da wasu manyan mutane da dama.

Tsarin mulkin da Najeriya ke bukata - Dantata

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya aiko ta'aziyya yayin da aka rasa daya daga cikin dattawan Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dantata ya goyi bayan kiraye-kirayen kafa tsarin gwamnati na Fira Minista a matsayin mafita ga matsalolin Najeriya.

Fitaccen dan kasuwar, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 15 ga watan Faburairu a Kano lokacin da ’yan Majalisar Wakilai suka ziyarce shi.

Akalla ‘yan majalisar tarayya 60 ne suka gabatar da bukatar yin gyara ga kundin tsarin mulk na1999 na ficewa daga tsarin mulkin shugaban kasa zuwa tsarin Firayin Minista.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.