Ministar Tinubu Ta Ware N290m Domin Sanya Fitilu a Karamar Hukumarta

Ministar Tinubu Ta Ware N290m Domin Sanya Fitilu a Karamar Hukumarta

  • Ministar al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, ta ware Naira miliyan 290 domin samar da fitulu masu amfani da hasken rana a ƙaramar hukumarta
  • Za a gudanar da aikin ne a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina inda nan ne mahaifar Hannatu Musa Musawa
  • An kuma tanadi Naira miliyan 98 domin samar da wani babban tanti na Najeriya a wajen bikin fina-finai na Cannes wanda za a yi a ƙasar Faransa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja- Ma’aikatar fasaha, al’adu ta tarayya ta ware Naira miliyan 290 domin samar da fitilu masu amfani da hasken rana a ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.

Hakan yana ƙunshe ne a cikin kasafin kuɗin ma’aikatar na shekarar 2024 da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa hannu a watan Janairun wannan shekara.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa Kwankwaso, Atiku da Peter Obi ba za su kai labari ba a zaɓen 2027"

Za sanya fitilun N290m a Musawa
An ware N290m a kasafin ma'aikatar al'adu domin sanya fitulu a Musawa Hoto: Hannatu Musa Musawa
Asali: Facebook

Hannatu Musa Musawa wacce ke jagorantar ma'aikatar ta al'adu ta fito ne daga ƙaramar hukumar Musawa a jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuɗin da za a kashewa ma'aikatar al'adu

Har ila yau, ma'aikatar ta ware Naira biliyan 3.7 domin "bincike da ci gaba", da kuma Naira miliyan 98 na "babban tantin Najeriya" a bikin fina-finai na Cannes da za a yi a ƙasar Faransa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

An kuma ware Naira miliyan 150 ne domin “teburin bayanan al’adun gargajiya” a filin jirgin sama na Abuja da kuma Naira miliyan 26 domin abubuwan walwala, tallace-tallace da sauransu.

Fitilu za su ci N440m a shekarar 2024

Rahoton Fij.ng ya bayyana cewa ma'aikatar za ta kashe N440m wajen samar da fitilu a shekarar 2024.

Shugaba Tinubu ya ƙirƙiro ma'aikatar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira domin haɓaka tattalin arziƙin fikira.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7, sun kwato makamai masu yawa a Kaduna

Batun korar Hannatu Musawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan ƙorafin da aka shigar kan ministar al'adu, Hannatu Musa Musawa.

Kotun ta yi fatali da ƙarar da aka shigar kan Musawa dangane da muƙaminta na minista saboda matsalar rashin yin bautar ƙasa.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a, James Omotosho ya bayyana cewa masu ƙorafin sun gaza kawo shaidu masu karfi kan shari'ar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel