Hallaccin ‘Mining’: Abin da Malamin Musulunci Ya Ce Game da Notcoin da TapSwap

Hallaccin ‘Mining’: Abin da Malamin Musulunci Ya Ce Game da Notcoin da TapSwap

  • Bayan fashewar wani 'mining' da aka yi mai suna notcoin (NOT), 'yan Najeriya maza da mata, babba da yaro sun raja'a a kan harkar
  • Wannan ya jawo tambayoyi suka yawaita kan matsayin mining a addinin musulunci saboda mutane na tsoron cin kudin haram
  • Babban malamin addinin musulunci, Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ba da fatawa a kan mining inda ya bayyana cewa ya hallata a shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A makon da ya gabata, duniyar crypto ta cika da labarin fashewar wani 'mining' da aka yi mai suna notcoin (NOT), wanda aka ƙaddamar a kan fasahar gudanarwar 'blockchain' na The Open Network (TON).

Farfesa Mansur Isa Yelwa ya yi magana a kan hallaccin mining
Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ba da fatawa kan mining. Hoto: Univers Business, Professor Mansur Isa Yelwa
Asali: Facebook

An shiga harkar mining gadan-gadan

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

Matasan Najeriya da dama sun samu makudan kudi daga wannan notcoin din, abin da ya jawo dumbin mutane suka raja'a kan harkar mining gadan-gadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na baya-bayan da da ake yi shi ne TapSwap, wanda kamar notcoin, a Telegram ake yin shi ta hanyar daddana wani hoto da ke bayyana a manhajar shi.

Wannan ya jawo matasa, maza da mata suka fara neman ilimi da kuma halaccin yin 'mining' a addinin Musulunci domin gujewa cin kudin haram.

Farfesa Mansur ya yi magana kan mining

A wani faifan bidiyo da @el_uthmaan ya wallafa a X, an ga babban malamin Musulunci, Farfesa Mansur Isa Yelwa yana ba da fatawa a kan mining.

Sai dai malamin ya ce zai bayar da fatawar ne daidai gwargwado fahimtar da ya yi wa mining daga bayanin da masu tambayar suka yi masa, tun da ba shi da masaniya a kansa.

Kara karanta wannan

Harajin tsaron yanar gizo: Pantami ya magantu da CBN ya fitar da sabuwar sanarwa

Bayan sauraron bayani daga wani matashi, ga abin da malamin ya ce game da mining din Notcoin da su TapSwap.

"Mining ya halatta" - Farfesa Mansur

Farfesa Mansur ya fara da cewa idan har ma'anar mining shi ne wani ya sa ayi masa aiki, misali wannan da mutane ke tara lambobi domin ya biya su, to mining ya halatta.

"Dalilin da ya sa na ce mining ya halatta shi ne: Musulunci ya halatta harka ta ijara, ma'ana ka sa wani aiki kai kuma ka biya shi ma damar bai sabawa musulunci ba.
"Ijara ta na fadawa kan yin aiki a biya ka ko da kai da kake yin aikin ba ka san kima da darajar aikin da kake yi ba, kamar dai mining, lambobin ba su da amfani da wajenka amma haka kamfanin ya ji ya gani ya ce ka tara masa.
"Tun da harka ce ta 'almal', ma'ana duk abin da ya ke da kima da daraja a wurin mai shi, kuma kuka yi yarjejeniya na yin aikin, to a fahimtata, mining ya halatta tunda almal ne."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Babbar mota ta murkushe motoci 4, mutane da yawa sun mutu a jihar Imo

A karshe Farfesa Mansur Isa Yelwa ya ce matasa su ci gaba da mining.

Kalli bidiyon a kasa:

Tinubu ya gana Alhaji Dantata

A wani labarin, mun ruwaito cewa hamshakin dan kasuwar Arewa da ke a jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja.

Duk da cewa ba a san dalilin wannan ziyarar ba, amma mun ruwaito cewa wannan ne karo na farko da Dantata da Tinubu suka hadu bayan rantsar da shugaban kasa a Mayun 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel