Aisha Umaru, bahaushiyar farko da ta fara shiga shirin BBNaija ta fara shan suka
Shigar 'yar arewa mai suna Aisha Umaru, wacce aka fi sani da Kaisha, shirin BBNaija ya janyo cece-kuce daga ma'abota kafafen sada zumuntar zamani.
A yayin shiga shirin, Kaisha ta sanar da jagoran shirin, Ebuka Obi-Uchendu cewa ita mutum ce mai nasara amma tana da raunin zuciya.
Ta kara da yin alkawarin dawo da barkwanci cikin gidan tare da bayyana halayyanta na gaskiya.
Kaisha ta kasance 'yar kasuwa daga jihar Sokoto.
Sai dai kuma wasu 'yan Najeriya na ganin cewa bai dace a ga 'yar arewa a wannan shirin ba. Amma kuma wasu na jinjinawa masu zaben da suka zabi Kaisha.
Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Saleem, ya bayyana cewa ya matukar jin takaicin ganin mace 'yar arewa daga jihar Sokoto a gidan.
Matashin, a jerin wallafar da yayi a shafinsa, ya ce babu namiji mai hankali da zai bar diyarsa mace ta shiga wannan shirin.
Ya kara da cewa, yana mamakin daga yankin arewan da matashiyar ta fito.
KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: An yi musayar kalamai tsakanin ministan Buhari da dan majalisa
"Babu dan arewa mai hankali da zai bar diyarsa ta shiga shirin BBNaija. Ina mamakin daga wani bangare na arewa take.
"Idan dai har da gaske Aisha Kaisha 'yar arewa ce. Toh a gaskiya ba kabilar Hausa/Fulani bace don an sansu da kunya, kuma shigar mutunci na cikin al'adarsu," ya wallafa.
A wani labari na daban, wasu hotuna masu matukar bada mamaki na tagwaye maza da suka yi aure rana daya ya bayyana.
Tagwayen sun aura mata tagwaye a rana daya kuma sun haifi tagwaye kowannensu a rana daya.
'Yan biyun maza masu kama daya an gano sunayensu Sa'ad da Sa'id kuma an ga hotunansu dauke da jariransu.
A yayin da Legit.ng bata tabbatar da sahihancin labarin da ya bayyana tare da hotunan mazan da 'ya'yansu ba, hotunan sun ci gaba da bai wa jama'a sha'awa.
A hotunan masu matukar bada sha'awa da suka karade shafukan sada zumuntar zamani, sabbin iyayen sun rike kyawawan 'ya'yansu cike da kauna.
An gansu su kansu sanye da kaya iri daya da kuma huluna iri daya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng