Don girman Allah a dakatar da shirin BBNaija - Malamin coci ya roki FG
- Babban malamin cocin Epiphany da ke Abuja ya roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin Big Brother Nigeria (BBNaija)
- Akunna ya kara da cewa yadda 'yan Nigeria ke mayar da hankali wajen kallon shirye shirye irin BBNaija, babbar ila ce ga tarbiya da al'adunsu
- Malamin cocin ya kuma roki gwamnati da ta dawo da martabar al'adu da darajar ilimi a Nigeria
Ven. Ifeanyi Akunna, babban malamin cocin Epiphany da ke Abuja ya roki gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirin Big Brother Nigeria (BBNaija) da sauran shirye shirye makamantansa.
BBNaija wani shiri ne da ake gabatarwa na rayuwar zahiri, inda mutanen cikin shirin ke killace a gida daya na tsawon wani lokaci, kuma ana bayar da kyautar makudan kudade.
Akunna ya yi wannan kiran a cikin wani sako da ya yi wa take: "Gidan da aka bude shi don alfasha', sakon da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja.
Ya ce ire iren wadannan shirye shiryen suna cusa rashin tarbiya da ruguza alkunyar da ke tsakanin matasan Nigeria.
Malamin cocin ya kuma roki gwamnati da ta dawo da martabar al'adu da darajar ilimi a Nigeria.
Akunna ya kara da cewa yadda 'yan Nigeria ke mayar da hankali wajen kallon shirye shirye irin BBNaija, babbar ila ce ga tarbiya da al'adunsu.
KARANTA WANNAN: Gwamna Masari ya kaddamar da babban kamfani a jihar Katsina
Akunna ya jaddada cewa Shaidan ne kawai ya ke fitsari a zukatan mutane da har suke iya kallon shirin, wanda ake nuna tsiraici da lalata karara, hakan kuwa kaucewa dokokin Allah ne.
"Duk masu kallon wannan shirin na BBNaija sun kauracewa hakan kuma su roki Allah gafara saboda yin hakan ya kaucewa koyarwar ubangiji, kuma yana lalata tarbiya.
"Ire iren wadannan shirye suna bada gudunmawa wajen bata tarbiyar al'umma, da kuma makomarsu a nan gaba."
Ya yi kira ga hukumar kula da kafofin watsa labarai ta Nigeria (NBC) da kuma hukumar sa ido kan shirye shirye ta Nigeria (NCDMB) da su haramta shirin da ma sauran shirye shirye irinsa.
Akunna ya yi takaicin yadda kafofin watsa labarai da nishadi suka manta irin illolin dake tattare da irin wadannan shirye shiryen.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng